Zaɓen Amurka: Ƴan Democrats na zargin shirin yin kutse

Manyan shugabannin jam'iyyar democrats a Amurka sun buƙaci hukumar FBI ta yi masu bayani kan abin da suka ce manyan ƙasashen waje na ƙoƙarin yin katsalandan a zaben watan Nuwamba da ke tafe.

Shugabar majalisar wakilian Amurka Nancy Pelosi da kuma jagoran ƴan Democrats Chuck Schumer a majalisar dattiajai, sun bayyana damuwa cewa ana ƙoƙarin amfani da majalisa domin yada labaran karya.

A cikin wata wasika da suka aikawa wa hukumar FBI, shugabanin Democrats ɗin sun bayyana damuwa kan barazanar da suka ce ke tattare da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.

Sun ce barazanar ta kunshi wani yunkuri na ƙaddamar da wani kamfen na kokarin yada wata farfagandar karya.

Shugabar majalisar wakilaoi Nancy Pelosy da kuma Sanata Schumer sun ce ya zama wajibi hukumar FBI ta yi wa dukkanin mambobin majalisar bayani kan bayanan sirri game da barazanar kafin karshen watan Yuli.

A cikin wata sanarwa, Joe Biden babban mai hamayya da shugaba Trump a zaben shugaban ƙasa ya ce ba zai ji shakkar daukar mataki ba kan duk wata kasa da ta zabi ta yi shisshigi a siyasar Amurka.