Babu dalilin yin kira ga Amurkawa su rika sanya takunkumi - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai ga wani dalili da zai sa ya bukaci yan kasar su rika sanya takunkumi ba.

Kafin a ga Mr Trump da takunkumi a baya-bayan nan, ya jima yana adawa da sanya shi, duk da matsin lambar da yasha daga masu bashi shawara da kuma yan adawa.

Yayin wata hira da kafar talabijin ta Fox ranar Jumma'a, Trump ya ce kamata yayi a bar kowanne dan kasa ya wataya kamar yadda dokar kasa ta bashi dama.

Yana magana ne kwana guda bayan da babban likitan da ke jagorantar yaki da cutar a Amurka Dr Anthony Fauchi, ya yi kira ga yan siyasa da jagorori su ci gaba da kira ga mabiyansu, su rika sanya takunkumi.

Wannan na faruwa ne yayin da aka sanar da miliyoyin yara yan makaranta a kasar cewa za su cigaba da kasancewa a gida ba tare da komawa don fara sabon zangon karatu ba.

Dalilin da mahukunta suka bayar kuwa shine yadda ake cigaba da samun yaduwar cutar korona a kasar.

A jihohi biyu mafi yawan jama'a wato California da Texas, sama da yara miliyan goma sha daya da suka dogara da makarantun gwamnati ba za su koma don cigaba da karatu nan da wasu makonni ba.

Ita kuwa jihar Texas na shirin soma aiwatar da tsarin karatu daga gida har nan da watan Nuwamba.

Yanzu haka dai adadin masu cutar a Amurka ya haura miliyan uku, kana ana samun karuwar masu harbuwa.

Kwanan baya Dr Anthony Fauchi ya yi gargadin cewa adadin masu kamuwa na iya kaiwa dubu dari a kullum nan ba da jimawa ba, kuma a yanzu akan samu akalla sama da mutum dubu saba'in da ke kamuwa a kowacce rana.

Kasar ce kuma ke kan gaba, a jerin kasashen cutar tafi kama jama'a a duniya, yayin da kasar Brazil mai sama da mutum miliyan biyu ke biye mata baya.

Adadin wadanda cutar ta kashe a Amurkan ya kai 141,924.