Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Trump ya haramta wa 'yan kasashen Turai shiga Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabbin ka'idojin hana shiga kasarsa kan Turai, a yunkurinsa na yaki da yaduwar coronavirus.
Amma ya ce matakan "masu karfi kuma wadanda suka zama dole" ba za su shafi Burtaniya ba, wacce ke da mutum 460 da suka kamu da cutar.
Wata sanarwa da aka fitar daga Fadar White House ta bayyana dalilan da suka sa aka haramta wa matafiya daga kasashe 26 kawai a Turai shiga Amurkar.
Wannan yasa haramcin bai shafi wasu kasashen Turai ba, cikinsu har da Ireland.
"Don hana sabbin masu dauke da cutar shigo wa kasarmu, za mu haramta wa 'yan kasashen Turai shigowa," in ji Mista Trump ranar Laraba.
"Sabbin dokokin za su fara aiki ne da tsakar daren Juma'a," a cewarsa. Haramcin ba zai shafi 'yan asalin Amurka ba.
Kawo yanzu, an samu mutum 1,135 masu dauke da cutar a fadin Amurka, inda 38 suka mutu.
Mista Trump ya ce Taryyar Turai ta "gaza daukar irin matakan" da Amurka ta dauka don yaki da cutar.
Shugaban na Amurka ya sha suka bisa matakan da ya dauka a kan cutar ta covid-19.
A lokacin da suke mayar da martani kan jawabinsa, manyan 'yan Democrat sun ce kalaman nasa na da daga hankali kuma abin mamaki ne yadda Shugaba Trump bai yi komai ba kan rashin kayan gwaje-gwajen cutar a Amurka.