Duniya na fargabar ƙarancin jama'a nan da shekara ta 2100

jariri

Asalin hoton, Getty Images

Raguwar da ake samu ta haihuwar alamu ne da ke nuna tsukewar yawan al'umma a kusan kowacce kasa kafin karshen karni.

Kasashe 23 - ciki har da Spain da Japan - ana sa ran yawan 'yan kasashen zai zabtare ya dawo rabi a shekara ta 2100.

Al'ummar kasashe za su tsofe sannu a hankali, inda galibi mutane za su kasance daga masu shekaru 80.

Short presentational grey line

Me ke faruwa ne?

Alkaluman yara da ake haifa - yawan jarirai da ake sa ran akalla mace ta haifa - ya yi kasa.

Idan kuwa adadin haihuwa ya ragu da kashi 2.1 cikin 100, to yawan al'umma ya soma yin kasa kenan.

A 1950, haihuwar da mata ke yi a rayuwarsu na kai a kalla yara 4.7 cikin 100.

Binciken da Jami'ar Washington ta gudanar ya nuna cewa adadin yaran da ake haifa ya ragu da kashi 2.4 a shekara ta 2017 - sannan binciken da suka wallafa a Mujallar Lancet ya nuna cewa alkaluman zai sake kasa da kashi 1.7 a shekara ta 2010.

bbc

Sakamakon hakan, masu bincike na sa ran yawan mutane a duniya zai kai kololuwa wato biliyan 9.7 a shekara ta 2064, sannan ya fado ya koma biliyan 8.8 a karshen karni.

Wannan babban al'amari ne; duniya na sauyawa yawan al'ummarta na raguwa saboda wasu dalilai da mutane suke assasawa,'' a cewar wani kwararren mai bincike Ferfesa Christopher Murray a zantawarsa da BBC.

"Ina ganin wannan yanayi na tattare da sarkakiya haka kuma akwai bukatar sake nazari, mu sauya salon tsarin da muka dora al'umma a kai."

Wannan layi ne

Me yasa haihuwa ke raguwa?

Matsalar ba ta da alaka da yanayin maniyin namiji ko kuma tunanin da zai iya fadowa a zuciya idan aka dauko batun haihuwa.

Ana dai alakanta faruwar haka da samun karin wayewa na ilimi da aiki ga mata, da kuma shan magungunan hana daukar ciki, wanda ke bai wa mata zabi idan suna son haihuwa ko takaita yaran da za su iya haifa.

A galibin lokuta raguwar da ake samu na haihuwa na tattare da labari ko bayanan masu gamsarwa.

Wannan layi ne

Kasashen da rashin haihuwa zai fi tasiri?

  • A Japan kiyasi ya nuna cewa yawan al'ummar kasar zai ragu daga miliyan 128 zuwa kasa da miliyan 53 a karshen karni
  • Italiya ma za ta fuskanci irin wannan yanayi, inda yawan 'yan kasar daga miliyan 61 sai dawo miliyan 28
  • Akwai kasashe 23 - da suka hada da Spain da Portugal da Thailand da Koriya Ta Kudu - da za su rasa sama da rabin al'ummarsu.
  • China a yanzu, ita ce kasa mafi yawan al'umma a duniya, ana sa ran yawan al'ummarta zai kai kololuwa a cikin shekaru 4 masu zuwa wato biliyan 1.4 kafin daga bisani su yi kasa su dawo miliyan 732 a shekara ta 2100. India za ta maye gurbinta
  • An yi hasashen adadin mutane a Burtaniya zai kai miliyan 75 a shekara ta 2063, sannan zai yi kasa ya koma miliyan 71 a 2100
  • Wannan zai kasance abin damuwa a duniya, inda a kasashe 183 cikin 195 yawan jariran da za ake haifa za su yi kadan wajen maye gurbin mutanen da ke mutuwa.

Mece ce matsalar?

Wani tsoho da jariri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan gaba kadan tsofaffi za su fi matasa yawa a duniya a cewar bincike

Ana iya tunanin cewa hakan abu ne mai kyau ga muhalli. Rashin yawan mutane na iya taimakawa wajen rage fitar da gurbatacciyar iska da sare bishiyoyi da rasa gonaki.

"Hakan gaskiya ne sai dai matsala ta shekaru (adadin tsoffi zai zarce na matasa) hakan kuma zai shafi daidaiton harkoki bisa ka'idar shekaru." A cewar Farfesa Murray.

Short presentational grey line

Binciken ya yi hasashe kamar haka:

  • Adadin yara masu shekaru kasa da biyar zai ragu daga miliyan 681 a 2017 zuwa miliyan 401 a 2010
  • Masu shekaru sama da 80 za su karu daga miliyan 141 a 2017 zuwa miliyan 866 a 2100.

Farfesa Murray ya ce: "Wannan zai haifar da gagarumin sauyi. Hakan ya sani damuwa saboda ina da yarinya 'yar shekara takwas tunanina shi ne ya duniya za ta kasance a wannan lokacin."

Tsoffi za su koma biyan haraji kenan? Wa zai biya wa tsoffi kudin kula da lafiyarsu? Wa zai bai wa tsoffi kulawa? Za a ke yi wa mutane ritaya a aiki?

"Muna bukatar tsarin ceton-kai tun da wuri," a cewar Murray.

Wannan layi ne

Ya Afrika za ta kasance?

Ana sa ran yawan al'umma a Kudu da Hamadar Sahara ya rubanya adadin da ake da shi yanzu zuwa sama da biliyan uku a shekara ta 2100.

Binciken ya kuma ce Najeriya za ta kasance kasa ta biyu mafi girma a duniya, inda yawan al'ummarta za su kai miliyan 791.

Masana na ganin a wannan lokacin 'yan Afirka za su kasance su suka fi yawa a galibin kasashen duniya.

"Wannan kuma zai yi tasiri domin zai zama babban kalubale kan batun nuna wariya ga bakar-fata, domin bakaken fata za su yi mamaya", a cewar Farfessa Murray.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne