Abu 10 da kuke buƙatar sani game da yawan al'ummar Najeriya

Mutanen Najeriya
Bayanan hoto, Ana hasashen nan da shekara 80 yawan al'ummar Najeriya zai kai miliyan 728

Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ware ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara a matsayin Ranar Yawan Jama'a Ta Duniya.

Sakon MDD na bana dangane da ranar shi ne jan hankalin duniya kan batutuwan da ba a kammala cimma su ba wadanda aka amince da su a babban taronta na 1994 kan Yawa da ci gaban Al'umma.

Ana hasashen nan da shekara 80 yawan al'ummar duniya zai nunka, inda kasashe kamar Najeriya da ke da mutum muliyan 200 a yanzu, za ta kai kasa mai yawan mutum miliyan 728.

Yadda yawan 'yan Najeriya ya yi ta karuwa cikin shekara 40. . .

BBC ta yi duba kan wasu abubuwa 10 da watakila ba ku sani ba dangane da yawan al'ummar Najeriya.

  • Yawan al'ummar Najeriya a yanzu ya kai 206,214,251 kamar yadda bayanan Majalisar Dinkin Duniya suka nuna
  • Yawan jama'ar Najeriya ya kai kashi 2.64 cikin 100 na jumullar al'ummar duniya
  • Najeriya ce ta bakwai a jerin kasashen da suka fi yawan jama'a a duniya
  • Mutum 226 ke zaune a duk fadin murabba'in kilomita
  • Yawan fadin kasar Najeriya ya kai murabba'in kilomita 910,770
  • Kashi 52.0 cikin 100 na al'ummar kasar na rayuwa ne a birane, inda bayanai suka nuna cewa akwai mutum 107,112,526 da ke rayuwa a birane a shekarar 2020
  • Matsakaicin shekarun 'yan Najeriya shi ne 18
  • Hukumar kidayar jama'a ta Amurka ta ce yawan al'ummar Najeriya zai zarta na Amurkar a shekarar 2047, inda a lokacin yawan mutanen Najeriya zai kai miliyan 379.25 million. A lokacin Najeriya za ta zama kasa ta uku mafi yawan jama'a a duniya
  • MDD ta ce manyan dalilan da ke sa yawan jama'ar kasar ke karuwa su ne auren wuri da yawan haihuwa da rashin samun damar yin tsarin iyali
  • Duk mutum 1,000 suna haihuwar 37 a Najeriya.
BBC
Hasashen yawan jama'ar Najeriya

Nan da shekara 30

  • 206,139,589Yawan jama'a a shekarar 2020

  • 262,977,337Yawan jama'a a shekarar 2030

  • 329,066,615Yawan jama'a a shekarar 2040

  • 401,315,000 Yawan jama'a a shekarar 2050

Source: Majalisar Dinkin Duniya
Birane 10 da suka fi yawan jama'a a Najeriya. . .