Cibiyar nukiliyar Iran: Me ke jawo hare-haren ban mamaki a Iran?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Jiyar Gol
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Fasha
- Lokacin karatu: Minti 4
A ranar 30 ga watan Yuni, na karbi wani sako ta email daga wata kungiya da ke ikirarin kai hare-hare, mai suna Homeland Cheetahs.
Kungiyar ta ce ta kai hari kan cibiyar nukiliyar Iran da ke Natanz. A sakon mai kunshe da bayanai kungiyar ta yi ikirarin tarwatsa muhimman abubuwan da gwamnatin Iran ba za ta iya boyewa ba.
Kungiyar ta ce mambobinta sun kunshi mutane da ke adawa da gwamnatin a cikin dakarun Iran da jami'an tsaro, sannan su suke kai akasarin hare-hare da mahukunta Iran ke boyewa.
Nan take na garzaya shafin yada labaran gwamnatin Iran da sauran sahihan kafofin sada zumunta, amma babu inda naga an ambaci wadanan hare-hare.
Sa'o'i da samun wannan, hukumar da ke kula da makamashi ta Iran ta sanar da wani fashewa da aka samu a cibiyar nukiliya ta Natanza, sai dai ta yi watsi da batun hari aka-akai.
Kwana guda da faruwar hakan, majalisar koli ta tsaro a Iran ta sanar da cewa ta san abin da ya haddasa ''fashewar'' a Natanz amma ''saboda dalilai na tsaro'' har yanzu babu wani karin bayani kan abin da ya haddasa fashewar.
Hotunan da aka dauka ta tauraron Nasa ya nuna cewa an kai hari da misali 02:06. Bayanan da aka tattara sun yi daidai da wadanda maharan suka ka aika mun a sakon email.
Sakonin da kungiyoyin suke aike wa tsararru ne, sannan suna kunshe da bayanan bidoyo na farfaganda kan hare-haren da aka kai a yankunan daban-daban da ke wajen Iran.
Shirya irin wadannan bayanai da bidiyo na bukatar lokaci, ba wai 'yan sa'o'i ba wajen shirya su. Duk wanda ya ba da umarni akansu to yana da masaniya kan fashewar da aka samu a Natanz tun kafin aukuwarsa.
Amma kuma mai yiwuwa ne watakil sakon email din wani kokari ne na batar damu ko sanin ainihin harin, sannan yana iya zama aikin jami'an kasashen ketare da ke adawa da gwmanatin Iran.
'Dakile hare-hare'
Kungiyar da ake kira, Homeland Cheetahs kusan daya suke da kungiyar nan da ke ayyukan ta'addancinta ta kafar intanet, kamar Persian Cat ko Charming Kitten - rukunin masu kutse ne da ake da yakinin wani bangare ne na dakarun juyin-juya hali na Iran.
Ba abun mamaki ba ne idan aka ce Homeland Cheetahs na da alaka da Persian Cat.

A karshen watan Mayu, hukumar da ke kula da tsaron intanet ta Isra'ila ta ce kasar ta dakile wani babban shirin kai mata harin intanet, wanda take zargin Iran din.
Kwanaki da yin hakan, aka kai harin intanet a Shahid Rajaae, wani muhimmin wurin kasuwanci da cibiyar zirga-zirga jiragen ruwa da ke kudancin Iran.
Sama da kashi 50 cikin 100 na harkokin Iran ta ruwa a wannan yankin ake gudanar da su. Harin ya haddasa ballewar ruwa da toshe hanyoyi saboda ambaliya.
Jami'ai a Iran sun daura alhakin hakan kan karancin wutan lantarki, ammam jami'an leken asirin yammaci sun san cewa akwai hannun Isra'ila a harin wanda tamkar ramako ta yi kan Iran din.
Hare-hare da Gobara
A cikin makonni uku da suka gabata an samu karuwar hare-haren ban mamaki da suka tarwatsa muhimman wurare a Iran.
An samu tashin gobara da dama da suka lalata kayayyaki a cibiyar nukiliya, matatun mai da cibiyar samar da wutan lantarki, kamfanoni da wuraren kasuwanci a fadin kasar.

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Daga ranar 26 ga watan Yuni zuwa yanzu ga wasu abubuwan da suka faru:
- Ranar 26 na Yuni: An samu fashewa a wurin samar da man da ake amfani da shi a makami mai linzami a Khojir, kusa da Parchin na Tehran; gobara a cibiyar wutan lantarki ta Shiraz, hakan ya haddasa rashin wuta
- Ranar 30 ga watan Yuni: Wani hari a asibitin Tehran ya yi ajalin mutum 19
- 2 ga watan Yuli: An samu fashewa da gobara a cibiyar nukiliya ta Natanz
- Ranar 3 na Yuli: Gobara ta mamaye Shiraz
- 4 ga watan Yulu: An samu fashewa da gobara a cibiyar samar da wutan lantarki da ke Ahwaz.
Saeed Aganji, wani dan asalin Finland ne da ke aikin jarida a Iran ya ce akwai abin mamaki yadda abubuwa ke faruwa watakil da gangan aka tsara hakan.
''Kai irin wadanan hare-hare a wurare masu muhimmanci a Iran, kokari ne na durkusar da tattalin arzikin Iran da kuma tilastawa gwamnati daina daukan nauyin kungiyoyin mayaka da sauya matsayinta kan gabas ta tsakiya.''
Parchin da Khojir sansanonin dakarun Iran ne wanda kuma ake ganin ake hada nukiliya da makami mai linzami a gabashin Tehran.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Hukumar da ke sa ido kan makamkin nukiliyar Iran ta kasa da kasa ta jima tana hana samun damar shiga Parchin, inda ake zargin Iran na aiwatar da manyan kwaje-kwaje da ke da alaka da kera makamin nukiliya.
Gargadin Iran
A wani yanayi na martani, kafar yada labaran Iran ta ce gobarar da ta tashi a Natanz watakila ba ta rasa nasaba da ''makarkashiya irin ta kasashen da ke adawa da ita, kamar Isra'ila ko Amurka''.
Babban jami'in farar hular Iran ya sha alwashi ''mayar da martani'' inda bincike ya tabbatar ana amfani da intanet wajen kai harin kasar.

Asalin hoton, Getty Images










