Hajji 2020: Shin wajibi ne taɓa Ka'aba lokacin Hajji da Umara?

Asalin hoton, Getty Images
Burin duk wani Musulmin da ya je aikin hajji shi ne ya taɓa ka'aba ya yi addu'o'i ya kuma mika kokensa ga Ubangij.
Sai dai a bana an yi tunani ba ma lallai a yi hajjin ba saboda annobar korona, amma kwatsam a watan da ya gabata Saudiya ta tabbatar za a yi Hajjin amma bisa wasu sharuda.
A ranar litinin an wayi gari da wadannan sharudan na hukumomi a Saudiya wanda daga ciki akwai haramta taba Ka'aba.
Sharudan da hukumomin suka fitar musamman haramta taɓa Ka'aba kusan shi ne abin da al'ummar Musulmi ke ta diga ayar tambata a kai, da kuma yadda hakan zai shafi ibadar wadanda aka amince ko za su samu damar sauke farali a bana.

Wajibi ne taba Ka'aba?

Asalin hoton, Getty Images
A tattaunawar da BBC ta yi da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce abubuwan da ake yi wa Ka'aba guda biyu ne dama, akwai zagayeta da kuma taɓa Hajar al-Aswad da Rukn al-Yamani.
Wadannan wurare biyu an sunnanta taɓa su ko sumbata, sannan a inda Hajar al-Aswad ya ke ana son mutum ya sumbace shi ko ya taɓa da hannu ko sujada ko kuma a yi amfani da sanda wurin nuna shi, in ji Daurawa.
''Idan kuma aka samu akasi na cunkosa ko wani dalili tun da wuri ne da mutane ke burin taɓawa sosai, sai a yi amfani da dan 'yatsa a nuna shi.''
Sheikh Daurawa ya ce ''babu wanda ya ce taɓa ka'aba wajibi ne a musulunci bayan wandanan wurare guda biyu da kuma Multazzam wato daidai kofar ka'aba.
''Multazzam kuma wuri ne da ake son idan mutum zai yi addu'a ya rungumi wurin ya fada wa Ubangiji bukatunsa.''
A cewar Sheikth Daurawa, dukkan wadanan wurare guda uku babu wanda ya zamo cikin rukunan aikin Hajji ko farilar hajji, kawai dai yana cikin sunnoni, idan ka yi zaka samu lada.
''Saboda cunkoson ganin yadda milyoyin mutane ke zuwa hajji da zagaye ka'aba aka baka damar cewa idan akwai cunkosa ko cutuwa to ka nuna shi daga nesa ka ce Allahu Akbar.
''Kowa na da dama guda biyu idan baka iya taɓa ko wadanne wannan wurare ba to ka nuna su dan 'yatsa ka yi kabbara ka wuce.''

Muhimmancin taba Ka'aba - Sheikh Daurawa
- Sunna ce mai karfi ta Mazon Allah SAW - yana taɓa Hajar al-Aswad kuma ya sambace shi
- Sahabai sun yi koyi da Annabi SAW wajen sumbatar Hajar al-Aswad
- Akwai lokacin da Sayyadina Umar yake cewa ''nasan kai Hajar al-Aswad dutse ne baka da ikon ka cuci mutum ko ka amfane shi, ban da na ga manzon Allah SAW ya taɓa ka ko sumbace ka ba zan sumbace ka ba''
- Taɓawa ku sumbatar Hajar al-Aswad na tattare da lada amma dai ba farila ba ce
- Idan akwai lalurori ko cunkoso nuna wa dan 'yatsa ya wadatar kamar yadda shari'a ta tanadar

Asalin hoton, Getty Images
Ingancin Hajji
Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce, ''da a ce an hana taɓawa an kuma hana nuna shi da dan 'yatsa to sai a ce an hana sunnoni guda biyu''.
Rashin taɓa Ka'aba ba zai shafi ingancin ibadar duk wani mutum da ya je aikin Hajji ba.
Taɓa wa ko rashin taɓa ka'aba ba shi da alaka da ibadar mutum, a cewar Daurawa
Malamin ya ce rukunan aikin Hajji su ne dawafi daga dakin Allah da Safa da Marwa da daukar niyya daga mikati sannan ka yi tsayuwar Arfa.
Wadanan rukunai su ne idan ba a yi su ba Hajji bai cika ba, don haka idan aka taɓa daya daga cikin wadanan to aikin Hajji ya fuskanci tasgaro
Baya ga wadanan duk sauran sunnoni ne kawai ko ba a yi su ba babu damuwa.

Karin bayani

Asalin hoton, Getty Images
Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin Hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can. Sai dai a baya can mazauna Saudiyya suna yin aikin Hajji ne kawai duk bayan shekara biyar.
Duk wani wanda zai yi Hajji a bana sai an yi masa gwajin cutar korona kafin ya fara aiki, sannan za a killace ka bayan an kammala aikin da kuma sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.
Za a rinka gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-kadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna. Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.
Ba za a bar mutanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba, kuma a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.












