Yadda aka 'yantar da birrai da ake bautar wa

Chained monkey climbs tree

Asalin hoton, Getty Images

Wasu shagunan sayar da kayayyaki da dama sun cire duk wani abun da aka samar da ruwan kwakwa daga kantinan bayan da aka gano cewa an hada man da kuma ruwan kwakwar ne da 'ya'yan itatuwan da birrai suka yi wahalar tsintowa.

An dai dauke birran daga daji inda aka ba su horo kan yadda za su tara kwakwa har 1,000 duk rana, a cewar wata kungiyar kare hakkin dabbobi ta Amurka, Peta.

Kungiyar ta ce a Thailand, ana yi wa birran da ake kira macaque a Turance kallon masu aikin dauko kwakwa.

A martaninsa, kamfanonin Waitrose, Ocado, Co-op da Boots sun yanke shawarar sayar da wasu kayayyaki.

A wani bangaren kuma, kamfanin Morrisons ya ce tuni ya cire kayayyakin da aka yi su da ruwa ko man kwakwar da birrai suka kado daga kantocinta.

Cikin wata sanarwa, Waitrose ya ce "a wani bangare na tsarin kula da walwalar dabbobi, mun yanke cewa da saninsu ba za su taba sayar da kayan da birrai ne suka aikatu a kai ba."

Co-op kuwa cewa ya yi: "a matsayinmu na masu tsari, ba za mu bari a yi amfani da gumin birrai ba wajen samo mahadin kayayyakinmu ba."

Cikin wani sakon Tuwita ranar Juma'a, budurwar Firaministan Burtaniya Carrie Symonds mai rajin kare gandun daji, ta yi kira ga shaguna da su guji sayar da kayayyakin.

Daga bisani Sainsburyya shaida wa BBC cewa: "Muna sake nazari tare da bincike game da lamarin da masu samar mana kayayyaki."

Shi kuma Asda ya ce: "Muna fatan masu ba da kaya su kiyaye ka'idojin samar da kayayyaki a kowane lokaci kuma ba za mu lamunci cin zarafin dabbobi ba." Ya sha walshin cire wasu samfurin kayayyaki daga kan kantocinsu har sai ya yi bincike kan zargin cin zarafin.

Ms Syonds, a shafinta na Tuwita ta yi kira ga Tesco da ya dauki irin wannan alkawarin: "Gareka Tesco! Don Allah kai ma ka daina sayar da irin wadannan kayayyakin," in ji ta.

Mai magana da yawun Tesco ya fada wa BBC: "Ba ma amfani da kayayyakin da birrai suka sha wahalar samarwa wajen hada madara da kuma ruwan kwakwa sannan kuma ba ma sayar da kayayyakin da kungiyar Peta ta yi ayar tambaya a kansu.

"Ba ma lamuntar haka kuma za mu daina sayar da duk wasu kaya da aka san birrai ne suka wahala wajen samo su,"

Daukar kwakwa 1,000 duk rana

Peta ta ce ta gano gonaki takwas a Thailand inda birrai suke kado kwakwa domin fitar wa zuwa sauran duniya.

A cewar Peta, birrai maza na iya daukar kwakwa 1,000 a rana. Ana tunanin dan adam zai iya daukar kwakwa 80.

Kungiyar ta kara da cewa ta gano "makarantun birrai" inda ake horar da dabbobi su dauki 'ya'yan marmari da tuka keke ko kuma wasan kwallon kwando domin nishadantar da baki masu yawon bude ido.

"Dabbobin da ke wadannan wurare - wanda akasarinsu an kama su ne ba bisa ka'ida ba tun suna jarirai - na nuna wasu dabi'u na cewa sun gaji sosai," kamar yadda Peta ta fada.

Monkey chained to a tyre

Asalin hoton, Getty Images

"Ana kulle birrai a jikin tsofaffin tayoyi ko a karamin keji wanda ba ya isarsu su wataya."

"An hangi wani biri cikin keji da aka dora saman wata budaddiyar babbar mota yana giriza kenjin a kokarinsa na tserewa da kuma wani biri mai ihu da ke kulle yana kokarin guduwa daga mai kula da shi."

A wata kara, an fada wa kungiyar cewa za a cire hakoran birran matukar suka yi kokarin cizon masu kula da su.

"Daraktar kungiyar ta Peta Elisa Allen ta ce "ana hana wadannan dabbobi masu hankali damar motsa jiki da abokantaka da sakewa da duk wani abu da zai inganta rayuwarsu duk don a yi amfani da su wajen tara kwakwa,"

"Peta na kira ga jama'a da su guji goyon bayan wahalar da birrai ta hanyar kin sayen duk wasu kayayyaki da suka danganci kwakwa daga Thailand."