Ko cutar korona ce ta kashe giwaye 350 a Botswana?

An kasa gano dalilin mace-macen ɗaruruwan giwaye da ba a saba gani ba a Botswana cikin wata biyu da suka gabata.

Dr Niall McCann ya ce abokan aikinsa a kasar ta kudancin Afrika sun gano fiye da gawawwakin giwaye 350 a gabar Kogin Okavango tun farkon watan Mayu.

Babu wanda ya san dalilin da ya sa giwayen ke mutuwa, kuma har yanzu ba a samu sakamakon gwajin samfur dinsu da aka dauka makonni kadan da suka gabata ba, a cewar gwamnati.

Botswana ce kasa ta uku a Afrika da yawan giwayenta ke raguwa.

Gargadi: Hotunan da ke cikin labarin nan ka iya ɗaga wa wasun ku hankali

Dr McCann, wani jami'i a wata Cibiyar Jin Kai ta ceto Gandun dazuzzuka, ya shaida wa BBC cewa da farko masu kula da gandun daji na yankin ne suka gaya wa gwamnati halin da ake ciki a farkon wata Mayu, bayan su hau jirgi sun zagaye saman kogin.

''Sun ga gawawwakin giwa 169 a zagayen da suka yi a jirgin na tsawon sa'a uku,'' a cewarsa. ''Tsawon lokacin da aka dauka ana duba tare da kirga gawawwakin abu ne da ba a saba ba.

''Wata daya bayan nan, ana kara gano wasu gawawwakin a binciken da aka ci gaba da yi, inda jumullarsu ta haura 350.''

''Wannan wani abu ne da ba a saba gani ba na yawan giwayen da ke mutuwa a lamarin da ba shi da alaka da fari,'' a cewarsa.

A watan Mayun, gwamnatin Botswana ta ce ba farautar giwayen aka yi ba - saboda ganin cewa ba a cire haurensu ba.

Akwai wasu dalilan da suka fi kama da na farauta.

"Kawai dai giwayen na mutuwa ne, babu wani abu bayan haka," in ji Dr McCann. "Idan da mafarauta ne suka yi amfani da wani sinadari don kashe su, to da an ga wasu dabbobin daban da suka mutu.''

Dr McCann ya kuma ce ba guba suka ci suka mutu ba, kamar irin yadda ya faru a Botswana a bara inda giwaye 100 suka mutu sakamakon cin guba.

Amma dai an kasa gane ko gubar ce ta kashe su ko kuma wata cuta daban. Yanayin yadda giwayen suka mutu ya nuna cewa da yawan sun fadi ne rub da ciki - kuma ganin su da aka yi suna tafiya a zagaye ya nuna cewa akwai yiwuwar ko wani abu ne yake shafar yanayin jikinsu, a cewar Dr McCann said.

Sai dai duk da cewa ba a san ainihin dalilin mutuwarsu ba, ba a cire yiwuwar cewa ko wata cuta da ke damun 'yan adam ce ta shafe su ba - musamman idan musabbabin cutar a ruwa ne ko a kasa.

Dr McCann ya ba da misali da annobar cutar Covid-19, wacce aka yi amannar ta faro ne daga jikin dabbobi.

"Bala'i ne na gandun dabbobi - amma akwai yiwuwar ya zama annoba ta lafiya," a cewarsa.

Sai dai ba su san abin da yake jawo dalilin mutuwar tasu ba.

"Mun aika samfur don yin gwaji kuma muna dakon sakamakon nan da makonni biyu masu zuwa ko fiye," in ji shi.