Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli yadda giwaye ke makokin rashin 'yan uwansu
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wannan bidiyon na wasu giwaye da suke bankwana da gawar shugabansu da ya mutu ya yadu kamar wutar daji a Sri Lanka.
Toron giwar ya mutu ne sakamakon fada da suka yi da 'yar uwarta.
Wannan al'amari ya zmo mai ban tausayi inda har sai da jami'an kula da gandun daji suka yi amfani da tartsatsin wuta wajen tarwatsa giwaye don a samu a binne gawar.