Ghana na bincike kan rusa ginin ofishin jakadancin Najeriya

Asalin hoton, Dele Momodu Twitter
Ma'aikatar wajen Ghana ta soma bincike kan rusa wani gina da ke ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar.
Ranar Asabar Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar.
Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, inda ya bukaci Ghana ta dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.
Mataimakin ministan wajen Ghana Charles Owiredu, ya shaida wa BBC Pidgin cewa "abin da ya faru abin takaici ne; Bai kamata mutum ya shiga ofishin jakadanci ba ba tare da an gayyace shi ba kuma Ghana ce take da alhakin kare lafiyar ma'aikatan difilomasiyya
A ranar Asabar ne aka wayi gari da ganin an rusa ginin ofishin jakadancin na Najeriya.
Mista Onyeama ya ce: "Muna yin tir da hare-hare biyu da masu aikata laifi da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gida da ke ofishin jakadancinmu a Accra, Ghana inda aka yi amfani da babbar motar rusa gini wajen rusa gidan," in ji Mr Onyeama.
Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.
Ya bukaci a bayar da cikakken tsaro ga 'yan Najeriya da kadarorinsu da ke Ghana.











