Sabuwar rayuwar mata bayan zaman sansanin mayu a Ghana

"Witch camps", like this one pictured in 2016, serve as havens for women linked to witchcraft

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sansanin mayu kamar irin wannan da aka dauki hotonsa a 2016, waje ne da ake kai matan da ake alakantawa da maita

Matan da aka zarga da maita a Ghana sun fara dawo da mu'amalarsu a cikin al'umma bayan da a baya aka keɓe su a wasu sansanoni.

An haramta keɓe wadanda ake zargi da maita a Ghana.

Ana yin zargin ne a wasu lokutan idan wani bala'i ya samu wani yanki. Kazalika ana zargin matan da ba sa bin dokar al'umma ma maitar.

Shugabannin al'umma ne suka ware sansanonin keɓe mutanen don samar da tudun mun tsira ga wadanda ake zargi da maita. Sai dai kuma ana takaita zirga-zirgarsu sosai.

Chilenja Bijabaye wata tsohuwa ce mai shekara 60 daga Naboli, a arewacin Ghana, da al'ummarta suka ki karbar ta bayan da ta kammala zama a sansanin da ke kusa da yankinta. Daga baya ɗanta ya gina mata gida a wani wajen daban.

"Mun tura mahaifiyarmu ga al'ummarmu sai manyan yankin suka ki yarda, suka ce idan dai aka zargi mutum da maita, to ba za ta iya komawa cikin al'ummar da zama ba.

''Ina son mahaifiyata ta rayu, don haka na yanke shawarar gina mata gida,'' kamar yadda ɗanta Njobo Azika ya shaida wa BBC.

Shekara biyar da suka gabata wata kungiya mai zaman kanta ta Action Aid tare da hadin gwiwar hukumar kare hakkin dan adam da wasu kungiyoyin suke aiki tare don rufe dukkan sansanonin da ke areacin Ghana, amma zuwa yanzu sun iya rufe kashi daya cikin uku ne kawai.