Kenya: 'An zarge ni da kama mijina ta hanyar maita'

Hoton Esther da Mijinta

Asalin hoton, Esther Kiama

Bayanan hoto, Esther Kiama ta kasance tare da mijinta tun lokacin da ya gamu da wannan lalura duk da bayan da abokansu suka juya musu
    • Marubuci, Daga Anne Ngugi DA Basillioh Mutahi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili

Esther Kiama na aiki ne a matsayin malamar makaranta a Nyeri da ke tsakiya kasar Kenya a lokacin da aka kira ta a waya aka ce mata maigidanta David ba shi da lafiya.

An shaida mata cewa ba karamin ciwo ne ke damun maigidan nata ba, daga bisani mutumin da ya kira ta a waya ya shaida mata cewa "Matsalar tabin hankali" ke damun mijin nata.

A lokacin a shekarar 2005 ne, Mrs Kiama ta shafe fiye da shekara ba ta ga mijin nata ba saboda ta koma wani gari domin ta fara kasuwanci.

A lokutan da take kai masa ziyara ba ta lura da cewa ba shi da lafiya ba.

To amma bayan da aka kirata aka shaida mata abin da ke faruwa, ba ta bata lokaci ba ta tafi nemansa.

Mrs Kiama ta shaida wa BBC cewa, " Sai da muka je gida muka same shi sannan aka fara masa magani".

Esther Kiama
Esther Kiama
I would leave him in the house and one day I found that he had burnt the ceiling"
Esther Kiama

Mrs Kiama ta ce maigidan nata " Yana magana da kansa ne a zuwan kamar yana magana da wani amma kuma ba kowa a wajen sai shi kadai".

Daga bisani Esther ta yi bayani a kan abin da aka gano a asibiti yana damunsa inda aka ce mata ai lalurar ta shafi kwakwalwarsa.

Ta ce: "Abin ya yi tsananin tun bayan da muka koma gida, akwai wata rana da dan fita na bar shi a gida shi kadai ko da na dawo na tarar ya kona rufin dakin da yake ciki, inda ya ce mini wai akwai wasu mugayen mutane da yake nema a saman rufin".

Ta ce ban fahmci abin da ke damun mijina ba, abu dai kamar an sanya wa mijina hannu.

Ganin yanayin jikin maigidan nata sai ta sake yanke shawarar cewa gara ta mayar da shi asibiti, to amma sai 'yan uwansa suka hana.

Har ma suka zarge ta da wai ta shanye mijin nata ne.

Ta ce "Mahaifinsa ya zo da kansa don ya dauke shi, sannan ya ce wai an shaida masa cewa dansa ba shi da lafiya, don haka ya zo saboda ya ga alamar kamar na 'kama' masa da ne".

Raba ta da mijinta tsawon shekara 15 abu ne da ya daga mata hankali ita da 'ya'yansu hudu.

Ta ce "Da farko na kadu, amma kuma ni mai imani ce, don haka na saddakar kuma na san cewa komai yana da karshe".

Ko da yake ba ta son ta ga kullum jikin maigidan nata na kara tsanani.

Bayanan bidiyo, What is a mental health problem?

Saboda imanin da sirikan Mrs Kiama suka yi cewa "na kama dansu ne, ma'ana ni mayya ce ba su nemi taimakon asibiti ba."

A lokuta da dama dai a kan alakanta matsalar da ta shafi kwakwalwa a Kenya da 'maita' ko kuma "baki", maimakon a nemi maganin abin.

Ma'aikatar lafiya ta Kenya ta ce, da yawan mutanen kasar ba sa neman maganin irin wannan lalura.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta kiyasta cewa ana samun mutum guda cikin hudu da yake da matsalar da ta shafi kwakwalwa.

Babu dai adadin masu irin wannan lalura a Kenya, amma kuma akwai bukatar mahukunta a kasar su yi wani abu don wayar da kai tare da magance wannan matsala.

Kusan shekaru, Mr Kiama ya zame wa iyayensa wani nauyi musamman ma mahaifiyarsa wadda dattijuwa ce kuma har ta fara rashin lafiya saboda bacin rai da kuma damuwa a kan rashin lafiyar danta.

Lokaci-lokaci, makota kan tuntubi Mrs Kiama a kan batun maigidanta.

Mrs Kiama ta ce "A wasu lokuta a kan kira ni a shaida mini cewa an ga maigidana ya na yawo a kan titi hakan ke sa ni na yi maza na je na nemo shi na mayar da shi gaban iyayensa".

Ta ce wani lokaci ma har dafa masa abinci nake na kai masa ya ci.

Amma duk da haka ba a daina zargin cewa na kama shi ba in ji Mrs Kiama.

line

Mece ce cutar tabin hankali ta bipolar disorder?

  • Akwai nau'uka daban-daban na wannan cuta ta bipolar da ta shafi kwakwalwa
  • Wadanda suke dauke da matakin farko na wannan cuta, za a ga suna fama da damuwa jefi-jefi
  • Wadanda ke a mataki na biyu kuwa, su kan yi fama da tsananin damuwa
  • Masu mataki na uku kuwa su kan shiga wani yanayi wanda idan an gansu kamar wasu marassa hankali
  • Idan mutum na mataki na karshe kuwa abin kan shafi kwakwalwarsu.
line

Mrs Kiama ta ce, abu ne mai wuya ka ga mutumin da kake matukar kauna na fama da irin wannan cuta ta tabin hankali.

Ta ce na yi fama da tsangwama da habaici daga wajen 'yan uwa da abokan arziki inda har wasu suka juya mata baya.

Wata malamar asibiti mai gashin kashi Maggi Gitu, wadda ta kware wajen hada aure, ta ce ba dai-dai ba ne a rinka kiran mai matsalar tabin hankali a matsayin mahaukaci.

Ta ce abin da masu irin wannan lalura ke bukata shi ne fahimta da kuma kula.

Mrs Maggie, ta kuma shaida wa BBC cewa, ya kamata a rinka zuwa asibiti akai-akai domin duba masu irin wannan lalura domin gano wacce irin matsala ce.

Ta ce gajiya da kadaici da fargaba da tsoro na janyo mutum ya samu kansa a cikin matsalar tabin hankali kamar na Mr Kiama.

Duk da irin yanayin da maigidan Mrs Kiama ke ciki ba ta guje shi ko wulakanta shi ba, duk kuwa da irin shawarwarin da kawayenta ke ba ta.

Ta ce "Na fada musu cewa saboda alkawari da rantsuwar da muka yi a lokacin aurenmu a coci, shi ya sa nake kula da mijina",

"Kai na fada muku gaskiya muna matukar kaunar junanmu, kuma 'ya'yanmu hudu da shi".

Esther Wanjiru Kiama
Bayanan hoto, Yanzu Esther Kiama ta nuna wa 'ya'yanta kada su ji tsoron mahaifinsu

A karshe dai, Mrs Kiama ta yanke shawarar cewa za ta je ta dauko mijinta daga hannun iyayensa.

Ta ce "Bayan shekara uku, na shaida wa 'ya'yana cewa za mu je mu sato babansu".

Tare da 'ya'yanta da kuma likitan kwakwalwa, sun yanke shawarar dauko mijinta daga gidan iyayensa.

Ta ce "Ko da muka je, faratan yatsunsa na kafa da hannu sun yi zaro-zaro ga dauda a ciki, sai da na dauki kwanaki ina gyara shi, na mishi aski saboda gashin da ke kansa da fuskarsa ya sa ya yi kamar dodo".

Mrs Kiama, ta ce sam ba a kula da shi a gidan iyayensa.

Bayan sun dawo gida, an kai Mr Kiama asibiti inda ka gano ainihin abin da ke damunsa, daga nan sai aka kwantar da shi a asibiti tsawon wata biyu.

Tun da aka sallame shi daga asibiti ya koma gida tare da matarsa, sai ya fara samun sauki, koda ya ke sai a hankali zai warke kwata-kwata.

Yanzu ya na tare da iyalansa cikin farin ciki.

Likitan da yake kula da shi ya bai wa matarsa da 'ya'yansa shawarar yadda za su rinka kula da shi.

line
In the Mind montage