Najeriya na son a kamo wadanda suka rusa ginin jakadancinta a Ghana

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    A nan muka kawo karshen abubuwan da muke kawo muku a wannan shafin. Amma za ku iya ci gaba da duba sauran labarai a bbchausa.com, sannan ku tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta.

    Kafin nan, ka kanun labaran da muka kawo muku a wunin yau:

    • An kama wanda ake zargi da kai harin Ingila -Firanministan
    • PDP ta amince Obaseki ya shiga zaben fitar da gwani
    • ·Sojoji suna zanga-zanga kan albashi a Somalia
    • An rusa ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana
    • Mataimakin gwamnan Ondo ya fice daga APC ya koma PDP
    • Dalilai 5 da ke ta'azzara annobar korona a Yemen

    Mu kwana lafiya.

  2. Najeriya na son a kamo wadanda suka rusa ginin jakadancinta a Ghana

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar da ke Accra, babban birnin Ghana.

    Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

    "Muna yin tir da hare-hare biyu da masu aikata laifi da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gida da ke ofishin jakadancinmu a Accra, Ghana inda aka yi amfani da babbar motar rusa gini wajen rusa gidan," in ji Mr Onyeama.

    Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.

    Ya bukaci a bayar da cikakken tsaro ga 'yan Najeriya da kadarorinsu da ke Ghana.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. An kama wanda ake zargi da kai harin Ingila

    PA MEDIA

    Asalin hoton, PA Media

    Firanministan Burtaniya Boris Johnson ya ce ya kadu da harin da aka kai a garin Reading da ya kashe mutun uku ya kuma jikkata wasu uku.

    Tuni an damke wanda ake tuhuma wato Khairi Saadallah wanda ya ake zargin ya kai harin da aka yi anfani da wuka.

    Rahotanni sun ce matsahin mai shekaru 25 dan Libya ne kuma sananne ne ga jami'an tsaro.

    Masu bincike sun ce ba su tunanin harin na hadin baki ne.

  4. Sojojin Somaliya da ke bore saboda gaza biyan su albashi sun tare kan titina a Mogadishu

    DALSAN TV

    Asalin hoton, DALSAN TV

    Wasu sojojin da ke bore a Somaliya sun tare babban titin da ke kusa da fadar shugaban kasar, a wani mataki na zanga -zanga saboda kin biyan su albashi.

    Wasu daga cikin sojojin sun ce sun shafe shekara daya ba tare da albashi ba.

    Wata kafar yada labarai ta kasar ta nuna wani hoton bidiyo yadda sojoji ke tare masu abin hawa daga dakarun kwantar da tarzoma na kungiyar Afrika daga wucewa.

    Sojojin ne dai ke fafatawa da mayakan al-Shabab masu tsattsauran ra'ayin addini, wadanda suka yi ikirarin daukar alhakin wasu tagwayen hare-hare da aka kai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai.

  5. Dalilai 5 da ke ta'azzara annobar korona a Yemen

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Annobar korona za ta iya yaduwa cikin gaggawa zuwa wurare masu nisa tare da yin mummunan tasiri na sanadin rayuka a Yemen sama da kowacce kasa a duniya, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

    Ga wasu daga cikin dalilan da ya sanya ta fadin hakan.

    1) Kasar har yanzu na fama da yaƙi: Tun 2015 Yamen ta fada cikin mummunan rikici, wanda ya janyo wa miliyoyin mutane rashin samun kulawar lafiya yadda ya kamata, babu ruwa mai kyau ga karancin tsafta a ko ina - wanda hakan zai kawo tarnaki kai tsaye ga yakin da ake da annobar.

    2) Tuni kasar na fama da matsalolin da suka shafi bil'adama mafiya muni a duniya: wanda yanayin da ake ciki zai iya haifar da cutuka masu yaduwa ga al'ummar kasar.

    3) Dama tsarin kiwon lafiyar Yemen ya rushe tuni: Yakin da ake yi ya kara durkusar da tsarin kiwon lafiyar kasar, abin da ya sanya ba za su iya shawo kan annobar korona ba.

    4) Har yanzu ba a san adadin masu cutar ba a kasar: Ba tare da sanin takamaimai su wanene masu cutar ba, yana da wahala a iya kare yaduwarta ko kuma shiri kan yawan masu dauke da ita a kasar da dama tana cikin matsalar tsarin kiwon lafiya.

    5) Su kansu ma'aikatan lafiya ba su da wata kariya: Tare da magani da za a rika bai wa marasa lafiyar, jami'an lafiyar na fama da karancin kayan kariya, kamar rigar da ake sanyawa lokacin aiki da takunkumin fuska da dai sauran kayan aikin da kan kare likitoci.

  6. Coronavirus: Halin da ake ciki a Latin Amurka

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Adadin mece-macen da aka samu a Brazil masu alaka da cutar korona sun kai 49,976 zuwa ranar Asabar, yanzu masu cutar sun kai 1,067,579 kuma ana zaton adadin zai zarce hakan saboda rashin wadatattun kayan gwaji.

    Amurka ce kawai ta fi Brazil yawan masu kamuwa da kuma wadanda suka mutu sanadiyyar Covid-19.

    Kwarru sun ce har yanzu cutar ba ta kai ƙololuwarta ba a kasar, cutar kuma na kai wa ga kauyukan karkara cikin gaggawa da kuma sauran yankuna.

    A gefe daya kuma Chile da sauran kasashen yankunan Latin Amurka cutar na ci gaba da yi musu barna, inda ta fitar da sanarwa a ranar Asabar za ta sanya wasu mutum 3,069 da suka mutu cikin wadanda suka rasa rayukansu dalilin cutar korona, tare da sanar da sake dabarun tunkarar annobar.

    Kasar na da masu cutar 237,00, in kuma aka kara wancan adadin mamatan kan wanda ake da shi za su kai 7,000 ba ki daya.

    A Mexico magajin garin birnin Mexico ya sanar da dakatar da shirin sake bude kasuwanni har sai yawan masu cutar ya ragu, yana cewa za a rufe jihar ruf har sai makon gobe.

    Mutum sama da 20,000 ne suka mutu sakamakon cutar kuma sama da 170,000 aka tabbatar na dauke da cutar.

  7. Masu korona na karuwa a yammacin Afrika

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Mai wasan barkwancin nan dan Senegal Samba Sine, wanda aka fi sani da Kouthia ya warke daga cutar

    Kasashen da yawa a yammacin Afrika na fuskantar karuwar masu korona:

    • A Cote d'Ivoire an samu rahoton kamuwar sabbin mutum 402 wanda ya kai adadin masu cutar a kasar 7,276 yayin da mutum 52 suka mutu bayan sanar da mutuwar wasu mutum 3.
    • Senegal kuwa ta sanar da mutum 144 wadanda sabbin kamuwa ne da cutar tare da kuma mutuwar mutu 3. Yanzu adadin masu korona a kasar ya kai 5,783 kuma 55 sun mutu.
    • An samu sabbin mutum tara masu korona a Nijar a ranar Asabar. yanzu mutum 1,035 ne ke da cutar a fadin Nijar, 67 kuma suka mutu.
    • Togo kuma mutum shida ne suka karu, kuma mutum 561 ne kawai ke da cutar a kasar sai dai tuni mutum 13 suka mutu.
    • A Benin mutum 53 ne sabbin kamuwa da cutar, duka mutum 11 ne suka mutu cikin 650 da aka tabbatar a kasar.
    • Kafafen yada labarai na cikin gida a Burkina Faso sun ruwaito mutum daya da ya kamu da cutar ta Covid-19. Yanzu dai mutum 902 ne duka suka kamu da cutar a kasar 53 kuma suka mutu sakamakonta.
  8. PDP ta amince Obaseki ya shiga zaben fitar da gwani

    Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta amince gwamnan jihar Edo Godwin Obasaki wanda ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki da ya tsaya takarar a zaben fitar da gwani da zai gudana nan gaba.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP ta ce la'akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta, Gwamna Obasaki na da damar tsayawa takarar fitar da gwani a zaben gwamna na jihar.

    Haka zalika kwamitin koli na PDP wanda shi ne ke kan gaba wajen tabbatar da bin tsarin jam'iyyar ya ce mataimakin gwamnan Philip Shu'aibu shi ma na da damar shiga a dama da shi wajen zaben zama mataimakin gwamnan.

    Kwamtin ya sanar da matsar da zaben fitar da gwanin na gwamnan jihar Edo da aka fara tsarawa zai gudana ranar Talata 23 ga watan Yunin da muke ciki zuwa ranar Alhamis 25 ga watan.

    A makon nan ne kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC a Jihar Edo ya tabbatar da cire Gwamna Godwin Obaseki daga cikin waɗanda za su yi takarar, abin da ya yi sanadiyyar komawarsa jam'iyyar adawa ta PDP.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Mutum bakwai sun mutu a wasu hare-haren bam da aka kai a Somalia

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Kungiyar al-Shabab ce ke yawan kai wa sojoji hari a kasar

    Akalla mutum bakwai ne suka mutu wasu da dama suka jikkata a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a kudanci da kuma tsakiyar Somalia.

    'Yan kunar bakin wake uku ne suka tarwatsa kansu a mota a daidai wurin duba ababan hawa na sojoji da ke jihar Galmudug, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku.

    Haka kuma a wani harin na daban, an ajiye wasu bama-bamai biyu a kofar gidan wani jami'in soji a Wanlaweyn, inda mutum hudu suka rasa nasu rayukan a wurin.

    Al-Shabab ce ta dauki nauyi kai harin Wanlaweyn, kamar yadda kafar yada labarai ta Somali Memo news ta bayyana.

  10. Zimbabwe: Za a kwace dukiyar wadanda suka kasa bayanin yadda suka tara ta

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Zimbabwe ta ce za a kwace kadarorin duk mutanen da ba za su iya bayanin yadda suka tara dukiyarsu ba, ko da kuwa kotu ya wanke su daga cin hanci da rashawa.

    Shugabar hukumar Loyce Matanda-Moyo ta bayyana sabon atisayen a matsayin muhimmiyar hanyar kididdige dukiyar masu wadatar kasar.

    Ta ce masu binciken nata za su yi aiki tare da hukumar gabatar da kararraki karkashin masu lura da halasta kudaden haram da kuma masu kula da manyan laifuka ta kasar.

    A ranar Juma'a aka kama ministan lafiyar kasar Obadiah Moyo game da zargin cin hanci darashawa.

    Amma an sake shi bayan ba da belinsa kuma zai koma kotu a karshan wata Yuli.

  11. Makomar Cavani, Meunier, Bailey, Jorginho, Jimenez, Drinkwater da Ceballos

    Juventus ta bi sahun Manchester United da Real Madrid da ke bukatar dan wasan gaba naWolvesda Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29. (Calcio Mercato, via Mail on Sunday)

    Dan wasan gaba na Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, da kuma dan wasan baya na Belgium Thomas Meunier, mai shekara 28, ba za su tsawaita kwantaraginsu ba daParis St-Germainzuwa 30 Yuni wanda ke nufin ba za su buga wa kulub din gasar cin kofin zakarun Turai ba da za a fara watan Agusta.(RMC, via Mail on Sunday)

    Chelsea, Manchester City da Manchester United na ribibin dan wasan Bayer Leverkusen Leon Bailey, mai shekara 22 wanda darajarsa ta kai fam miliyan 40.(Mail on Sunday)

    Chelsea ta yi watsi da tayin Juventus na musayar Jorginho, mai shekara 28, domin karbo dan wasan Bosnia-Herzegovina Miralem Pjanic, mai shekara 30, daga Juventus.(Calcio Mercato, via Sunday Express)(Calcio Mercato, via Mail on Sunday).

    Cavani

    Asalin hoton, Getty Images

  12. An rusa ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar da ke Accra, babban birnin Ghana.

    Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

    "Muna yin tir da hare-hare biyu da masu aikata laifi da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gida da ke ofishin jakadancinmu a Accra, Ghana inda aka yi amfani da babbar motar rusa gini wajen rusa gidan," in ji Mr Onyeama.

    Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.

    Ya bukaci a bayar da cikakken tsaro ga 'yan Najeriya da kadarorinsu da ke Ghana.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Spain ta sake maraba da masu yawon buɗe ido

    Sufaniya ta janye dokar ta-baci, inda ta sake buɗe iyakokinta ga masu ziyara daga akasarin kasashen Turai sannan ta bar masu yawon buɗe ido na Birtaniya sake shiga kasar ba tare da an killace su ba.

    Sufanita ta kwashe wata uku tana cikin dokar ta-abaci, daya daga cikin mafiya karfi da aka sanya a Turai domin dakile yaduwar annobar korona.

    Firaiminista Pedro Sánchez ya yi gargadin cewa dole mutane su bi dokokin kiwon lafiya sau-da-kafa, duk da sassauta dokar ta-bacin.

    Mutum 28,322 suka mutu sakamakon kamuwa da covid-19 a Sufaniya.

    An sanya dokar ta-baci ne ranar 14 ga watan Maris, kuma an kwashe makonni da dama ba tare da barin mutane sdu fita motsa jiki ba sannan ba a bar kanana yara su fita daga gidajensu ba.

    Kiyasi ya nuna cewa mutum miliyan 80 ne suke zuwa Sufaniya don yawon bude ido duk shekara, kuma kasar tana samun kasi 12 cikin dari na kudaden shigarta daga fannin yawon bude idon.

    Kiyasi ya nuna cewa mutum miliyan 80 ne suke zuwa Sufaniya don yawon bude ido duk shekara,

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutum miliyan 80 ne suke zuwa Sufaniya don yawon bude ido duk shekara
  14. Magoya baya ba su halarci taron kamfe na Trump yadda aka zata ba

    Shugaban Amurka Donald Trump ya gudanar da taron yakin neman zabensa na farko tun bayan da kasar ta sanya dokar kulle sakamakon barkewar annobar korona, a gaban mahalarta kalilan kan yadda aka saba gani.

    A farkon mako Mr Trump ya yi ikirarin cewa mutum kusan miliyan daya sun bukaci a ba su tikitin shiga wurin taron mai suna Bank of Oklahoma Center da ke garin Tulsa.

    Sai dai mutanen da suka halarci wurin ba su cika filin taron wanda ke daukar mutum 19,000 ba don aka ne aka bar shirinsa na yi musu jawabi a wajen filin.

    An yi ta bayyana fargaba kan yiwuwar gudanar da taron ana tsaka da annobar korona.

    Cutar korona na cikin batutuwan da Mr Trump ya yi magana a kansu, a jawabin da ya kwashe kusan awa biyu yana yi, inda mahalarta taron suka rika yi masa tafi a jihar ta Oklahoma, cibiyar masu goyon bayan jam'iyyar Republican.

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Za a sake buɗe harkokin kasuwanci a Saudiyya

    Ranar Lahadi Saudi Arabia za ta soma sassauta dokar hana fita da ta sanya a fadin kasar, a cewar ma'aikatar cikin gidan kasar, in ji jaridar Saudi Gazette.

    Za a soke dokar hana fita a duk fadin kasar, ciki har da biranen Makkah da Jeddah inda a halin da ake ciki ana barin su ne su fita kawai don sayen muhimman abubuwan bukata.

    Za a bar kasuwanni su sake budewa ko da yake dole su rika aiwatar da dokokin hana kamuwa da cutar korona, a cewar ma'aikatar.

    A wani bangaren, ma'aikatar birane da yankunan karkara ta ce za a sake bude wuraren yin aski da wuraren gyaran gashi na mata daga ranar Lahadi.

    Sai dai ba za a bar masu zuwa Umrah su shiga kasarsa sannan su ma jiragen kasashen duniya ba za su shiga ba.

    Saudi

    Asalin hoton, Twitter/@Saudi_Gazette

  16. Buɗewa

    Barkanmu da safiyar Lahadi. Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan lokaci.

    Muna fatan ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin wainar da ake toyawa a sassan duniya.

    Za mu kawo muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu.