'Ko wanda ya kawo korona Najeriya ba a ci zarafinsa kamar ni ba'

@jidesanwoolu

Asalin hoton, @jidesanwoolu

Bayanan hoto, Tuni mutum na farko na da ya fara kamuwa da cutar ta coronavirus a jihar Legas ya samu sauki kuma an sallame shi daga cibiyar kebe marasa lafiya ta Yaba

Mutumin da aka yi zargin shi ne na farko da ya kamu da cutar korona a Kano, Ambasada Kabiru Rabi'u ya ce yayata sunansa da gwamnatin jihar ta yi shi ne sanadin zagi da tsinuwa da kuma tsangwamar da aka yi ta masa.

Ya ce al'amarin ya yi matuƙar tayar masa da hankali. "Tun da aka soma maganar kobid-19 ɗin nan, ban taɓa jin an kama sunan wani mutum an faɗa ba."

A cewarsa har mutumin da ake zargin ya kawo annobar Najeriya, ɗan ƙasar Italiya. Har ya je asibiti aka gwada shi kuma aka tabbatar yana ɗauke da cutar, ba wanda ya bayyana sunansa, har zuwa yau, in ji Ambasada.

Kabiru Rabi'u ya faɗa ta cikin shirin BBC Media Action mai taken Mu Tattauna na wannan mako, cewa shin mene ne dalilin faɗar sunana, ana terere da ni?

"Har da faɗar sunana da adireshin gidana. Wannan abu ya ɓata min rai ya tayar min da hankali," in ji tsohon jakadan.

Tun da farko Ambasada Kabiru Rabi'u ya bayyana mamaki kan yadda gwamnan Kano a cikin jawabansa ya zarge shi da zuwa Kaduna, tare da zuwa ya gaggaisa da mutane kafin ya koma Kano.

Zargin da a cewarsa ba gaskiya ba ne.

Ya ce faɗar sunansa da gwamnatin Kano ta sa aka yi ne ya janyo suka da mummunar aibatawar da aka yi ta masa musamman a shafukan sada zumunta.

A ranar Asabar 11 ga watan Afrilu ne, hukumomi suka sanar da ɓullar annobar korona a Kano, wadda a yanzu ta fi kowacce jiha yawan masu cutar a arewacin Najeriya.

Kabiru Rabi'u ya ce: "Cutar korona ba ganinta ake ba, bare ka ce ka gan ta, ka je ka ɗauko. Shi kuma wanda yake da ita, ba wata kama (ta daban) yake da ita ba, saboda haka bari ka je ka ɗauka a wurinsa ".

Ya nanata cewa taƙamaimai babu masaniya kan inda ya ɗauki cutar, wadda ke ci gaba da yaɗuwa tun bayan sanar da ɓullarta ranar 27 ga watan Fabrairu.

@jidesanwoolu

Asalin hoton, @jidesanwoolu

An fara gano cutar korona ne a jikin wani ɗan ƙasar Italiya bayan ya sauka Najeriya ta hanyar filin jirgin sama na Murtala Mohammed daga Milan ranar 24 ga watan Fabrairu kafin ya tafi jihar Ogun.

Mutumin wanda ya shigo da coronavirus Najeriya ya warke daga bisani bayan jinyar kwana 23 a Lagos.

Ambasada Kabiru Rabi'u ya ce har yanzu babu wanda ya taɓa faɗar sunan wannan mutum, don a kare sirrinsa kamar kowanne maras lafiya.

Zuwa yanzu yawan masu cutar a Najeriya ya doshi 10,000, cewar alƙaluman hukumar daƙile cutka masu yaɗuwa ta ƙasar.

Ya ce duk makusanta da abokansa na arziƙi gami da mutane masu fahimta, ba su ji daɗin irin wannan cin zarafi da aka yi masa ba.

Ambasadan ya ce duk da yake ya mayar da lamarinsa ga Allah. Kuma ya ɗauki abin da ya faru a matsayin ƙaddara, amma bai yafe ba.

"Ban yafe musu ba! Dalili kuwa shi ne idan wani ya buga a shafukan sada zumunta, wani ya bayyana ra'ayinsa, to wannan zan iya yafewa.

Amma wanda ya zauna ya ƙirƙiri labaran bogi a kan abin nan, shi ne ban yafewa ba, cewar Ambasada Kabiru.

Tuni dai aka sallami tsohon jakadan daga cibiyar da aka killace shi bayan shafe sama da kwana 20 yana jinya a Kano.