Coronavirus: Gwamna Masari ya amince a buɗe masallatan Juma'a a Katsina

Asalin hoton, @GovernorMasari
Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bayar da damar ci gaba da sallar Juma'a a jihar bayan makonni da saka dokar kulle da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.
Sakataren Gwamnatin Jihar ne, Alhaji Mustapha Inuwa ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito Mustapha Inuwa yana cewa su ma al'ummar Kirista za su iya zuwa wuraren ibadarsu duk Lahadi da kuma tafiye-tafiye a tsakanin ƙananan hukumomin jihar.
Sai dai ya buƙaci jama'a da su su ci gaba da bin umarnin kariya kamar saka takunkumi da bayar da tazara da wanke hannaye da sabulu da kuma amfani da mai na sanitiser.
Ya zuwa daren Alhamis, hukumar NCDC ta ce mutum 358 ne suka harbu da cutar korona a Jihar Katsina, yayin da 14 suka rasu da kuma 51 da suka warke daga cutar.






