Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ki shiga gasar Hikayata ta 2020
An buɗe damar shiga gasar gajerun labarai ƙagaggu ga mata zalla ta shekara-shekara da BBC Hausa ke shiryawa - Hikayata.
Wannan ne karo na biyar na gasar ta mata zalla, wadda aka fara a shekarar 2016.
Gasar na karɓar ƙagaggun labarai da aka rubuta cikin daidaitaciyyar Hausa wadda kuma ta bi duka ƙa'idojin rubutu da aka amince da su a hukumance.
Yadda za ki shiga gasar
Don shiga gasar karanta cikakkun Ƙa'idojin Shiga Gasar Hikayata sannan ki karanta Sanarwa Game da Tsare Sirrin Masu Shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa
Za a aika labari ga wannan adireshin: [email protected] sannan ki tura wadannan bayanan game da kanki:
•Suna (ko sunaye ga masu aiko da labarin hadin-gwiwa)
•Lambar waya (ko lambobin wayar kowacce daga cikin masu aiko da labarin hadin gwiwa)
•Adireshi (ga masu turo labarin hadin gwiwa, adireshin kowacce)
•Adireshin email (ga masu turo labarin hadin gwiwa, adireshin email na kowacce)
•Gajeren tarihi (ga masu turo labarin hadin gwiwa, gajeren tarihin kowacce)
•Takaitaccen bayani game da labarin
Ba za a karbi labarinki ba, idan bai cika wadannan sharuɗɗa ba.
Za a buɗe shiga gasar da karfe 11.00 agogon Najeriya da Nijar ranar 1 ga watan Yuni, 2020.
Za a rufe gasar da karfe 12.00 agogon Najeriya da Nijar ranar 24 ga watan Agusta, 2020.
Idan kika turo da labarinki bayan wannan lokacin ba za a karba ba.
Gwarazan Hikayata na baya:
- 2016: Aisha Muhammad Sabitu
- 2017: Maimuna S Beli
- 2018: Safiyya Jibril Abubakar
- 2019: Safiyya Ahmed
Akwai kyautar kuɗi da lambar yabo ga waɗanda suka yi nasara.
Sai shekarun mace sun kai 18 za ta iya shiga Gasar Hikayata ta Mata Zalla.
Za a sanar da waɗanda suka yi nasara a taron karramawa na watan Disamba a Abuja kuma a wallafa labaransu a shafinmu na intanet a kuma watsa cikin shirye-shiryenmu na rediyo.
Don Karin bayani game da gasar latsa nan.