Hikayata 2019: Saurari labarin 'Ba A Yi Komai Ba' da ya zo na biyu

Latsa alamar lasifikar da ke sama ku sha labari

A karshen watan Oktoba ne gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai karo na hudu na shekarar 2019.

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ce ta zo ta biyu inda aka ba ta lambar yabo da kuma kyautar $1,000.

Kuma a wannan makon mun kawo muku labarinta wato 'Ba A Yi Komai Ba', wanda ta karanta da bakinta, kamar yadda aka ce waka a bakin mai ita ta fi dadi.