Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ceto matan Najeriya da aka yi safarar su zuwa Lebanon
Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya ya ce an dawo da mata hamsin kasar bayan an ceto su daga hannun mutanen da suka yi safarar su zuwa Lebanon .
Mr Geoffrey Onyeama ya ce an killace matan bayan komawarsu kasar ranar Lahadi domin a tabbatar ba sa dauke da cutar korona.
A cewarsa, bayan kammala zaman killacewa, hukumar da ke yaki da safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP, za ta gana da matan domin su bayyana mata irin halin da suka shiga.
A watan jiya, an ceto wata mata 'yar Najeriya da ke aikau a Lebanon bayan an sanya ta a shafin Facebook inda ake tallanta ga duk wanda zai iya sayen ta a kanr $1,000.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana safarar dubban 'yan Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afirka kowacce shekara.
Galibi ana yaudararsu ne ta hanyar yi musu alkawarin samar musu da ayyukan yi a kasashen Turai ko Asia, amma daga karshe su kare da zama 'yan-aiki ko kuma shiga karuwanci.
A bara, wani wakilin BBC Arabic wanda ya yi ɓad-da-kama a Kuwait ya gano cewa akwai kasuwar saye da sayar da 'yan-aikin gida wacce take ci gaba da bunkasa a kasar.
Ministan harkokin kasashen wajen Najeriya ya wallafa sakon Twitter inda ya gode wa gwamnatin Lebanon saboda taimakon da suka bayar na kudi da kayan aii wajen tabbatar da cewa an koma da matan da aka yi safarar su gida ranar Lahadi.
Kazalika, an koma da 'yan Najeriya 19, wadanda suka makale a Lebanon sakamakon dokar kullen da aka sanya aboda cutar korona, gida.
Shugabar NAPTIP, Julie Okah-Donli, ta ce an tsaurara tsaro a otal din da aka killace matan.
Ta kara da cewa gwamnati za ta taimaka musu da hanyoyin inganta rayuwarsu bayan sun gama zaman killacewa.
A cewar NAPTIP, an yi safarar akalla 'yan matan Najeriya 20,000 zuwa Mali inda aka tilasta musu shiga karuwanci a shekarar da ta wuce.
Ms Okah-Donli ta ce hukumarta tana hada gwiwa da ma'aikatar wajen kasar domin ganin an koma da dukkan matan da aka yi safararsu gida.