Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Mun gano dalilai 7 na mace-mace a arewacin Najeriya'
Tawagar ƙwararrun da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa yankin arewacin kasar domin bincike sanadiyyar mace-mace a wasu jihohin yankin ta ce ta kasa mace-macen gida bakwai kuma yanzu ta kusa kammala rangadin da take a jihohin, inda daga bisani za ta fitar da bayani.
Shugaban kwamitin Dr Nasiru Sani Gwarzo ya ce kawo yanzu sun ziyarci jihohi shida daga cikin takwas da aka fuskanci mace-macen mutane a watan jiya.
Dr Gwarzo ya kuma sun gano abubuwa da yawa game da mutuwar ta farat ɗaya da mutane suka rinka yi a jihohin arewacin kasar.
"Mun je har makabarta inda muka kidaya kabarbarun mutane wasu mutanen kuma sun yi mana bayanai kan mamatansu. Amma kuma mun gano yadda a wasu jihohi an kambama mace-mace.
Mun samu samfurin mamata a jihohi da dama kuma muna jiran sakamakon abin da ya kashe su."
Shugaba Muhammadu Buhari ne dai ya tura tawaga ta musamman zuwa jihar Kano, inda aka samu karuwar mace-mace irin ta farat daya.
Sakamakon kuma samun irin mace-macen a jihohin Jigawa da Sokoto da Yobe da Borno da dai sauran jihohi arewacin kasar, sai shugaba Buhari ya fadada aikin kwamitin.