Jami'ai a Sudan ta Kudu sun ce ana fargabar daruruwan mutane sun mutu sakamakon rikicin da ya barke a jihar Jonglei da ke arewa maso gabashin kasar.
Cikin wadanda suka mutu har da ma'aikacin kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières.
Rikicin ya barke ne tsakanin makiyaya da manoma a kauyukan da ke karamar hukumar Pieri ranar Asabar, lamarin da ya kuma ya raba dubban mutane da gidajensu.
An kona gidaje da dama sannan aka sace kayan da ke wuraren ajiyar kayan abinci na hukumomin bayar da agaji.
Kazakila an sace mata da kananan yara da kuma dabbobi.
Jami'an tsaro sun ce sun gano makamai da dama, cikinsu har da bindigogi harbi-ka-gudu da bindigogin da ke sarrafa kansu da gurneti-gurneti daga bangarorin biyu.
Jami'an yankin sun ce suna ci gaba da tattara bayanai kan girman barnar da rikicin ya haddasa, ko da yake sun ce sun yi ammanar mutanen da suka mutu sun kai daruruwa tun bayan sabbin rikice-rikice da suka barke a yankin a watan Fabrairu.
Gidan rediyon Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya rawaito cewa mutum kusan 1,000 sun mutu a rikicin ko da yake ba a tabbatar da hakan ba.
Jihar ta Jonglei ta sha fama da rikici, lamarin da ya raba daruruwan dubban mutane daga gidajensu, baya ga tamowa da suke fama da ita.