Covid-19: Ganduje ya ɗauki ma'aikatan agaji a masallatai
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da wainar da ake toyawa a sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Nasidi Adamu Yahaya and Buhari Muhammad Fagge
Rufewa
A nan muke rufe wannan shafi inda muka wuni muna kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a duniya.
Ku leka kasa domin karanta labaran. Amma kafin nan, ga kanunsu:
'Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane'
Tsohon sojan da ke yaƙi da cutar korona a Ghana
COVID-19: Ana bincike kan 'yan China da suka shiga Najeriya
Cutar korona ta fi kashe masu kuɗi a Najeriya - Ministan Lafiya
'Yan sanda a Philippines sun kai samame wani asibiti da ba na ƙa'ida ba
Mu kwana lafiya.
Covid-19: Ganduje ya dauki ma'aikatan agaji a masallatai
Gwamnati jihar Kano da ke Najeriya ta ce masu bayar da agaji 1500 a masallatan Juma’a da ke jihar domin tabbatar da mutane sun bi shawarwarin da hukumomin lafiya suka bayar domin kaucewa yaduwar cutar korona.
Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya shaida wa BBC cewar gwamnati Kano ta bayar da umarnin rubata ka’idojin da likitocin suka bayar da Hausa da Ajami domin mutanen da ke karkara tare da bai wa limaman masallatan Juma’a makarin baki da hanci domin rabawa masalata.
Ya kara da cewa an umarci malamai da su takaita huduba da sallar a ranakun Juma’a da na Idi domin bai wa al’umma damar komawa gidajensu kafin cikar wa’adin da gwamnati ta bayar na zuwa masallacin.
A makon nan ne gwamnatin jihar Kano ta ce za ta bari a yi sallar Juma'a da Idi, matakin da wasu suke ganin tamkar tufka da warwara ne a yakin da ake yi da cutar korona.
Duka jihohin Amurka na yunƙurin sassauta dokar kulle
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Tuni shaguna suka fara budewa a jihar Florida
Bayan jihar Connecticut ta janye wasu daga cikin takunkuman da ta saka, kusan duka jihohin Amurka sun fara sassauta dokar kullen da suka saka bayan an shafe watanni biyu.
Sai dai akwai bambanci kwarai tsakanin yadda kowace jiha ke sassauta dokokinta.
Misali, Maryland ta bada dama ga mutane su je har bakin ruwa domin shakatawa, ita kuma Georgia ta bada dama ga wuraren aski su bude.
Sai dai har yanzu Gundumar Colombia bata bayyana batun ko za ta sassauta dokar ba.
A halin yanzu sama da mutum 92,000 suka mutu sakamakon cutar korona a Amurka.
Babban sufeton 'yan Sanda ya bukaci jami'ai su ba 'yan jarida hadin kai
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya bukaci 'yan sandan kasar su ba 'yan jarida da sauran ma'aikata masu muhimman ayyuka da suka hada da ma'aikatan lafiya haɗin kai.
Babban sufeton ya bada umarni ga 'yan sandan da su rinka mutunta ma'aikatan na musamman da suka hada da ma'aikatan kashe gobara da motocin daukar marasa lafiya.
Sai dai ya kuma ja hankali ga ma'aikatan da kada su yi wasa da damar da aka ba su ta zirga-zirga ta hanyar ɓata rawarsu da tsalle.
Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE
Iƙirarin Trump 'kan Hydroxychloroguine ba gaskiya ba ne'
Masu sa ido a kan amfani da magunguna sun ce ikirarin shugaban Amurka Trump cewa Hydroxychloroquine na maganin Covod-19 ba gaskiya ba ne.
Sun kuma gargadi mutane a kan shan maganin ba bisa shawarar likita ba inda suka ce zai iya haifar da ciwon zuciya.
Ku kalli bayanin Abdulbaki Jari, dan jarida mai sa ido a kan coronavirus.
Bayanan bidiyo, Ikirarin Trump kan Hydroxychloroguine ba gaskiya ba ne
Tanzania da Kenya sun amince su tattauna kan rikicin iyakoki
Asalin hoton, Reuters
Shugaban kasar Tanzania John Magafuli da kuma takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta sun amince da cewa ministocin kasashen su hadu domin kawo maslaha tsakanin su kan wani rikici da ke faruwa a iyakokin kasashen biyu kan batun gwajin coronavirus.
A lokacin da yake jawabi a Singida, Mista Magafuli ya bai wa ministan sufuri na kasar da kuma kwamishinonin yankin garuruwan da ke iyakar kasar umarni da su tattauna da jami'ai daga Kenya domin kawo karshen duk wata matsala.
''Wannan lokaci ne na gina tattalin arziki, cutar korona ba a Afirka ta fara ba, bai kamata ta zamo silar kawo rikici a Gabashin Afirka ba," in ji shi.
Wannan na zuwa ne kwanaki hudu kacal bayan Mista Kenyatta ya rufe iyakar kasar da Tanzania inda aka hana komai shiga da fita banda kayayyakin da ke ratsa kasar suna wucewa.
Tattaunawa Kai-Tsaye da Gwamnan Zamfara
A yau da misalin karfe 09:30 na dare a agogon Najeriya za mu tattauna da Gwamnan jihar Zamfaran Najeriya Bello Matawalle @Bellomatawalle1. Ku aiko da tambayoyinku.
'Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane'
Jami'ai a Sudan ta Kudu sun ce ana fargabar daruruwan mutane sun mutu sakamakon rikicin da ya barke a jihar Jonglei da ke arewa maso gabashin kasar.
Cikin wadanda suka mutu har da ma'aikacin kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières.
Rikicin ya barke ne tsakanin makiyaya da manoma a kauyukan da ke karamar hukumar Pieri ranar Asabar, lamarin da ya kuma ya raba dubban mutane da gidajensu.
An kona gidaje da dama sannan aka sace kayan da ke wuraren ajiyar kayan abinci na hukumomin bayar da agaji.
Kazakila an sace mata da kananan yara da kuma dabbobi.
Jami'an tsaro sun ce sun gano makamai da dama, cikinsu har da bindigogi harbi-ka-gudu da bindigogin da ke sarrafa kansu da gurneti-gurneti daga bangarorin biyu.
Jami'an yankin sun ce suna ci gaba da tattara bayanai kan girman barnar da rikicin ya haddasa, ko da yake sun ce sun yi ammanar mutanen da suka mutu sun kai daruruwa tun bayan sabbin rikice-rikice da suka barke a yankin a watan Fabrairu.
Gidan rediyon Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya rawaito cewa mutum kusan 1,000 sun mutu a rikicin ko da yake ba a tabbatar da hakan ba.
Jihar ta Jonglei ta sha fama da rikici, lamarin da ya raba daruruwan dubban mutane daga gidajensu, baya ga tamowa da suke fama da ita.
Asalin hoton, Getty Images
Falasdinawa 'za su kawo karshen yarjejeniya da Isra'ila'
Wani babban jami'i a gwamnatin Falasdinawa ya ce an kafa kwamiti da zai
gabatar da bayanan cewa Shugaba Mahmoud Abbas ya kawo karshen duk wata
yarjejeniya da ya taba kullawa da Isra'ila.
Ranar Talata Mr Abbasa ya sanar da cewa ya dauki wannan matakin ne saboda
shirin Isra'ila na mamaye wasu yankunan Gabar Tekun Jordan.
Wakilin BBC ya ce ''Mr
Abbas ya jaddada warware duk wata yarjejeniya da Israi'la da Amurka, kuma idan
dai har hakan ta tabbata, matakin zai shafi yarjejeniyoyin da aka kulla shekaru
da dama da suka wuce wanda hakan zai yi tasiri kan rayuwar Falasdinawa musamman
mazauna Gabar Tekun Jordan.''
Ko a baya shugaban ya
taba irin wannan furuci duk da bai aiwatar ba, to amma a cewar wakilin BBC a
wannan karon akwai alamun da gaske yake yi.
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon sojan da ke yaƙi da cutar korona a Ghana
Wani
tsohon soja mai shekaru 95 a Ghana na yin tafiyar kilomita uku a kullum kuma
zai rika yin hakan tsawon mako guda, domin samar da kudin yakar cutar korona.
Private Joseph Hammond na son amfani da tallafin wurin
taimakawa sauran tsoffin sojoji a daukacin Afrika da cutar ta kama.
Akan haka ya yi kira ga shugabannin Afrika da su kara
zage dantse wurin yakar wannan cuta.
Shekarun Private Hammond 16, a lokacin da aka tura su
yaki a Burma.
Tsohon sojan ya ce takwaransa Captain Tom Moore na
Birtaniya ne ya ba shi kwarin gwuiwa, wanda ya samar da tallafi daga al'umma na
fam miliyan 32 ga hukumar lafiyar Birtaniya a dalilin kai koma da ya rika
yi a kullum a gadinarsa.
Asalin hoton, Guba
An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta manhajar Zoom
An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar manhajar bidiyo ta Zoom a Singapore, a yayin da kasar take ci gaba da zama a kulle sakamakon cutar korona.
An yanke wa Punithan Genasan, mai shekara 37, hukuncin kisan ne ranar Juma'a sakamakon samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi a shekarar 2011.
Wannan ne karon farko da aka yi amfani da manhajar Zoom wajen yanke hukuncin kisa a kasar.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana kisan a matsayin "abin kyama" a daidai lokacin da duniya take fama da annobar korona.
An dage galibin zaman kotu a Singapore zuwa ranar 1 ga watan Yuni, inda ake sa ran za a dage dokar kulle.
Asalin hoton, Getty Images
COVID-19: Ana bincike kan 'yan China da suka shiga Najeriya
Majalisar
Wakilan Najeriya ta kaddamar da bincike game da wasu 'yan kasar China da
gwamnatin ta kai kasar a watan jiya da sunan taimaka wa bangaren kiwon lafiya
wajen yaki da annobar korona.
A
baya-bayan nan dai ana ta ce-ce-ku-ce a kasar kan 'yan kasar ta China musamman
bayan da aka daina jin duriyarsu da kuma sanin aikin da suke yi a cikin
Najeriya.
Wasu
rahotanni a kasar ma na cewa wasu daga cikin 'yan Chinar, ma'aikatan gine-gine
ne ba likitoci ba, kuma hatta jami'an da ke yaki da cutar ta korona ba su da
cikakkiyar masaniyar inda su ke.
A
cewar wani dan majalisa, Abdulrazak Namdas, ya ce irin wadannan ce-ce-ku-cen da ake yi
na daya daga cikin dalilan da suka sa majalisar wakilan kasar ta
kaddamar da bincike domin gano gaskiyar al'amarin.
A makon jiya ne Ministan Lafiya na Najeriya, ya ce ba su san inda 'yan kasar ta China suka shiga ba, ko da yake daga bisani kamfanin gine-gine na kasar ta China da ke Najeriya ya ce suna tare da shi.
Asalin hoton, Getty Images
Cutar korona ta fi kashe masu kuɗi a Najeriya - Ministan Lafiya
Ministan Lafiya a Najeriya, Mr Osagie Ehanire, ya ce akasarin mutanen da cutar korona ta
halaka a kasar `yan boko ne da masu sukuni.
Mr Ehanire ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.
"Alkaluma sun nuna cewa akasarin mutanen da suka mutu sanadin cutar [korona] masu ilimi ne kuma attajirai wadanda ba sa zuwa asibiti sai jiki ya yi tsanani, bayan sun jarraba shan magani a gida abin ya gagara," in ji Ministan.
Ya yi
gargadin cewa mace-macen da ake yi ka iya munana, idan irin wadannan masu hannu
da shunin ba su bar dabi`ar jinkirta zuwa asibiti domin a yi musu jinya ba.
Minista Ehanire ya ce zuwa yanzu dai mutum 191 ne cutar korana ta yi sanadin barin duniya a
kasar.
A cewarsa, ko da yake har yanzu ba a samu mace-macen masu dauke da cutar a Najeriya sosai ba idan aka kwatanta da wasu kasashe, amma cutar za ta ci gaba da yaduwa a kasar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mr Osagie Ehanire ya yi kira ga 'yan Najeriya su saurari barkewar cutar korona sosai
DR Congo ta fara bincike kan kisan wasu 'yan aware
Asalin hoton, DRC Police /Twitter
Bayanan hoto, An kama Ne Muanda Nsemi, wanda ke jagorantar kungiyar a watan da ya gabata
Gwamnatin Congo ta ce ta fara bincike kan kisan wasu gwamman 'yan aware da jami'an tsaro suka yi a watan jiya.
Ministan kare hakkin dan adam Andre Lite ya ce ana zargin jami'an 'yan sanda da zuwa gidan shugaban 'yan awaren da ke jiran shari'a tare da kwashen dukiyarsa.
Kungiyar Human Right Watch ta ce jami'an tsaro sun yi amfani da karfin da ya wuce iyaka kan kungiyar Bundu Dia masu rajin farfaɗo da darajar masarautar Kongo mai cike da tarihi.
An kama Ne Muanda Nsemi, wanda ke jagorantar kungiyar a watan da ya gabata, bayan ya yi ikirarin shi ne shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a wani abu da ya kira juyin mulkin daga sama.
Wani fasto zai yi zaman kaso saboda karya dokar kulle
Asalin hoton, AFP/Getty Image
Wani Fasto na ƙarƙashin kulawar ma'aikatar shari'a a garin Burma da ke Myanmar, bayan ya gurfana gaban wata kotu bisa zargin karya dokar da aka sa saboda korona.
Fasto David Lah ya ci gaba da gudanar da tarukan addini a Yangon bayan gwamnatin yankin ta haramta gudanar da duk wani taron mutane a ranar 13 ga watan Maris.
Sama da mutum 70 ne aka gwada suna dauke da cutar bayan halartar taron addinin a Myanmar, kimanin kashi 40 cikin 100 da mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar a kasar.
Mista Lah ya ce babu mabiyin Yesu na gaskiya da zai kamu da cutar. Kazalika faston wanda mashahuri ne - shi ma ya yi fama da cutar ta korona, bayan gwajin da aka yi masa aka ga yana dauke da cutar.
Idan an kama shi da laifi, zai yi zaman jarum na shekara uku. Akwai mutum uku da ake tuhuma tare da faston.
'Yan sanda a Philippines sun kai samame wani asibiti da ba na ƙa'ida ba
Asalin hoton, Reuters
'Yan sanda a Philippines sun kai samame wani asibiti da kyamis da ke duba wasu 'yan kasar China da ake zargin suna da korona a boye, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito jami'an kasar sun bayyana.
An kama mutum biyu yayin samamen a cikin wani gida da aka mayar asibiti mai dauke da gado bakwai. An kuma samu wani mara lafiya daya a cikin ginin.
An samu wasu kayan da ake zargin na gwajin cutar korona ne sama da 200, an kuma samu tarin sirinji a sharar kauyen da gidan yake.
Wadanda aka kama ma'aikatan wani asibitin China ne da kuma wani mutum da ke tafiyar da kyamis din, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.
An kuma mayar da mara lafiyar da aka samu a wajen wanda dan ƙasar China ne ke zuwa wani asibiti da ke kauyen.
Asibitin dai na arewa maso yammacin birnin Manila ne, kuma an yi amannar ya dauki kimanin watanni uku yana aiki, in ji jami'an.
An rantsar da sabon Firaiministan Lesotho
Asalin hoton, Getty Images
An rantsar da tsohon ministan kudin Lesotho Moeketsi Majoro a matsayin sabon Firaiministan kasar, kwana guda bayan Thomas Thabane ya aje aikinsa.
Mista Majoro ya karɓi rantsuwar ne a fadar King Letsie III a safiyar yau Laraba.
Tsohon Firaininstan ya yi murabus ne biyo bayan matsin lambar da ya fuskanta kan zargin sa da hannu cikin kisan tsohuwar matarsa. Zargin da ya sha musantawa.
Sifaniya na son ƙara tsawaita dokar kulle
Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Sifaniya Pedro Sanchez ya nemi majalisar dokokin kasar ta kara tsawaita dokar kulle na tsawon mako biyu.
Pedro Sanchez ya ce babu wanda ke da ‘yancin dawo musu da hannun agogo baya game da nasarar da suka samu ta yaki da cutar korona.
Wannan zai zama karo na biyar kenan da ake kara tsawaita dokar tun daga watan Maris.
Madugun ‘yan adawa na kasar Pablo Casado ya ce Mista Sanchez na ikirarin ceton Sifaniya daga rikicin nda kuma shi ne ya kirkiri rikicin wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba a taba gani ba a duniya.
Jihar Nassarawa ta dage dokar hana taruwar jama'a na mako biyu
Asalin hoton, Facebook/ AA Sule
Jihar Nassarawa a Najeriya ta dage dokar hana taruwar jama'a na mako biyu inda daga bisani za a sake yi wa dokar duban tsanaki.
Kwamishinan Labaran jihar ne, Dogo Shammah ya bayyana hakan inda ya ce suna sa ran malaman addinai za su bi dukkan ka'idodjin da aka shimfida yayin taruwar jama'a domin gujewa kamuwa da cutar korona.
Sharuddan dai su ne masu ibada za su wanke hannayensu da sanya takunkumin fuska.
Wannan dagin dai na zuwa ne 'yan kwanaki kafin gudanar da salla da shagulgulan Idi.
Kenya ta kora bakin haure 182 zuwa Tanzania
Asalin hoton, EPA
Ma'aikatan lafiya na kasar Kenya sun musanta shigar 'yan kasar waje mutum 182 cikin kasar ta iyakokin kasar da Tanzania bayan ta tabbata cewa suna dauke da cutar korona.
Daga cikin 182 dai gwajin da aka yi musu a kan iyakar kasar ta Namanga mutum 126 na dauke da cutar ta korona. Ba a tantance kasashen 'yan kasar wajen ba.
Shugaba Uhuru Kenyatta ranar Asabar cewa kasar ta rufe iyakokinta da Tanzania da Somaliya sakamakon karin bazuwar cutar korona.
Ba a dai a hana manyan motocin kaya shiga kasar amma kuma dole sai an yi wa direbobin motocin gwaji