Coronavirus a Kano: Majalisar malamai ta yi ƙorafi kan buɗe masallatai

Majalisar malamai ta jahar Kano ta ce ya kamata a ce gwamnati ta yi nazari kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma'a da ta idi a jahar saboda yiwuwar fargabar yaduwar cutar korona.

Shugaban kungiyar Majalisar malaman a Kano, Mallam Ibrahim Khalil ya shaida wa BBC cewar duk da cewar gwamnatin jahar ba ta tuntube su ba a yayin yanke wannan hukuncin da ta yi, amma ya kamata ace ta yi la'akari da bukatar mutane.

Malaman Ibrahim Khalil, ya ce wajibi ne gwamnati ta kalli damuwar mutane da kuma abin da ya dace ga mutane tun da bata tuntubi majalisar malamai a kan matakin data dauka ba.

Ya ce " Amma irin wannan yanayi na annoba da ake ciki tun da har an bayar da umarnin zuwa sallar Jumma'a da ta Idi, to duk wanda yake jin tsoron cewar zai kamu da cutar ko kuma zuwa masallacin zai iya zame masa hadari don yana da wata lalura, to zai iya zamansa a gida".

Amma wanda kuma yake ganin shi zai iya zuwa masallacin ba tare da wata matsala ba, to shi wannan zai iya zuwa masallaci ya yi sallah in ji malamin.

Ya ce " Batun a rinka cewa duk wanda bai je masallaci ba ya aikata zunubi, to ba haka abin ya ke ba in dai har yana da kwakkwaran dalilin".

Matashiya

A ranar 18 ga watan Mayun 2020, ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aminci da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma'a da kuma Idi.

Wannan mataki ne bai yi wa majalisar malaman ta jihar Kano dadi ba saboda rashin tuntubarsu, koda yake malam Ibrahim Khalil ya ce an tuntubi wasu daga cikin malaman majalisar amma dai ba da sunan majalisar ba.

Duk da barin ayi sallar Jumma'a da ta Idi a Kanon, an umarci Malaman Masallatan Juma'ar da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cunkoso.

Gwamnatin jihar Kano dai ta bi sahun wasu jihohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma'a da na Idi.