Ana musayar yawu a Kano kan ma'aikatan lafiya masu korona

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya ta ce akalla ma'aikatan lafiya da likitoci 68 ne suka kamu da cutar korona a Kano kawo yanzu.
Kungiyar ta dai shaida wa BBC cewar akwai fargaba ganin yadda ake samun karin ma'aikatan lafiya a jahar da ke kamuwa da cutar, sakamakon rashin kayan kariya da suke fama da shi.
Shugaban kungiyar, Kwamared Ibrahim Mai Karfe ya ce ma'aikatan nasu na kamuwa da cutar ta korona ne saboda dalilai guda biyu - rashin kayan aiki da kuma boye bayanai da masu cutar ke yi lokacin da suka je asibiti ganin likita ba tare da snain suna dauke da cutar ta korona ba.
Kwamared Mai Karfi ya kara da cewa "maaikatan lafiya a jihar Kano za su kai 8 wadanda suka kamu da wannan ciwo na korona wato likitoci da sauran ma'aikatan lafiya."
Ya kara da cewa akwai rashin tuntuba tsakanin kungiyarsu da kwamitin yaki da cutar na jihar " ba sa tuntubar mu."
To sai dai babban jami'in kwamitin yaki da cutar a jihar, Dr Kabiru Hussaini ya ce alkaluman da kungiyar ta bayar ba haka suke ba "muna da kididdigar mutum 47 ba 68 ba kuma wadanda muke bayarwa su ne a hukumance kuma suke kan rijista watakila nasu alkaluman ba a tantance ba."
Tun a kwanakin bayanai ne dai shugaban asibitin Malam Aminu Kano da ke birnin na Kano ya shaida wa BBC cewa akwai ma'aikatan lafiya da likitoci fiye da 80 da ke jiran sakamakon gwajin annobar korona.











