Coronavirus: Adadin masu annobar ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Karin 'yan Najeriya kusan 400 ne aka tabbatar a ranar Jumma'a sun sake kamuwa da cutar korona, adadin masu cutar a daukacin kasar 3,912, in ji Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar.
A sakon tiwita da ta fitar daren Jumma'a, hukumar NCDC ta ce mutum 78 sun warke a cikin sa'a 24 da ta wuce, yanzu duka-duka wadanda suka warke daga annobar 679 a fadin kasar.
Jihar Legas, an sake gano mutum 176 da korona ta shafa, jihar ce annobar ta fi kamari kuma ta fara bulla a Najeriya, alkaluman NCDC sun ce yanzu jihar na da yawan masu korona 1,667.
Haka zalika, an ba da rahoton mutum goma sun sake mutuwa a cikin sa'a 24, abin da ya sa yawan mutanen da suka mutu sakamakon korona a Najeriya 117.
Wadannan ne alkaluma mafi yawa na mutanen da aka gano cutar ta shafe su da hukumomin Najeriya suka taba fitarwa cikin kwana guda a sama da wata biyu bayan bullarta cikin kasar.


Jihar Kano wadda ta fi yawan masu cutar a arewacin Najeriya, an sake gano mutum 65 ranar Jumma'a da suka kamu, yanzu adadin masu korona a jihar ya haura 500.
Jihar Katsina a wannan karon ita ce tazo ta uku a yawan wadanda suka kamu a ranar Jumma'ar inda mutum 31 suka sake kamuwa abin da ya kai adadin masu cutar a jihar yanzu 137.
Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar an sake samun mutum 20 da suka kamu da cutar, sai Borno 17, Bauchi 15, Nasarawa 14, Ogun 13 da kuma Plateau 10.
Jihohi irinsu Oyo da Sokoto da Rivers sun samu mutum hudu-hudu, sai Kaduna mai uku sai Edo da Ebonyi da Ondo masu biyu-biyu, sai kuma Enugu da Imo da Gombe da kuma Osun masu dai-dai.
Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.
Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da anobar kafin su warke daga bisani.
Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Jumma'a 8 ga watan Afrilu.
- Lagos-1,667
- Kano-547
- Abuja-336
- Ogun-113
- Osun-38
- Gombe-110
- Katsina-137
- Borno-142
- Edo- 67
- Oyo- 59
- Kwara-24
- Akwa Ibom-17
- Bauchi-117
- Kaduna-95
- Ekiti-12
- Ondo-15
- Delta-17
- Rivers-21
- Jigawa-83
- Enugu-10
- Niger-6
- Abia-2
- Zamfara-65
- Sokoto-93
- Taraba-15
- Benue-2
- Anambra-1
- Adamawa-15
- Plateau-15
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











