Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koriya Ta Kudu da Ta Arewa sun yi musayar wuta
Koriya Ta Kudu da Ta Arewa sun yi musayar wuta a yankin da ya raba kasashen biyu da aka haramta ayyukan soji.
Sojojin Koriya Ta Kudu sun ce wani harbi da Koriya Ta Arewa ta yi ya samu wajen da sojojinta suke gadi a garin Cheorwon da ke kan iyaka.
Ta ce ta mayar da martanin harbin tare da aike gargadi. Sai dai babu rahotannin jikkata.
Ba a saba ganin irin wadannan hare-haren a kan iyakar da aka fi tsaurara tsaro a duniya ba - lokaci na karshe da irin hakan ta faru shi ne a shekarar 2007.
Ba a san dalilin Koriya Ta Arewa na yin harbin ba.
Jami'an soji daga Kudu sun ce babu wata alama ta kai-kawon dakaru. Suna so su gano ko da gangan aka yi hakan ko kuma bisa kuskure ne.
Sharhi daga Laura Bicker, mai aiko da rahotanni daga Koriya Ta Arewa
Akwai 'yar yiwuwar cewa Koriya Ta Arewa da gangan ta yi hakan, a cewar sojojin Koriya Ta Kudu. Amma a wannan matakin ba a san ta yadda suka tattara bayanansu ba.
Ko da a bisa tsautsayi ko cikin sani aka yi, hakan ya nuna muhimmancin dakaru su dauke idonsu a yankin da aka cimma yarjejeniyar haramta ayyukan soji don tabbatar da cewa lamarin bai yi tsanani ba.
Idan kuma wani shiryayyen mataki ne daga Koriya Ta Arewa, to ya zama wani abu daban.
Lokacin da abun ya faru na da daukar hankali. Ya zo bayan sa'a 24 da bayyanar shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un a bainar jama'a bayan shafe kwana 21 ba a gan shi ba.
Kafar yada labaran kasar ta ce a watannin baya-bayan nan an yi ta yin atisayen soji a Arewa don kara zama cikin shirin ko ta kwana na yin yaki.
A shekarar 1953 bayan yakin Koriya ne aka samar da yankin da aka haramta ayyukan soji do samar da yankin zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
A cikin shekara biyu da ta gabata, gwamnatin Koriya Ta Kudu ta yi kokarin mayar da kan iyakar da aka fi tsaurara tsaro zuwa wani yanki na zaman lafiya.