INEC ba ta yanke shawarar dage zaben Edo da Ondo ba

Mahud Yakubu

Asalin hoton, INEC

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar dage zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo wanda aka tsara gudanarwa a ranakun 19 ga watan Satumba da kuma 10 ga watan Oktoban 2020 ba.

Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Litinin ta ce tun jadawalin zaben da ta fitar a ranar 6 ga watan Fabrairu, har yanzu kalandar na nan ba ta sauya ba.

Sanarwar ta ce yayin da hukumar ke kaffa-kaffa da mummunan tasirin da wannan annobar da ta dami duniya ke yi, haka kuma tana duba kokarin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi da hukumomin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki ke yi domin shawo kan wannan matsala.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Haka zalika hukumar ta cikin sanarwar ta ce idan akwai bukatar dage wannan zaben za a sanar ta hanyoyin da aka saba sanarwa a baya.

Cikin sanarwar Hukumar ta ce za ta ci gaba da bibiyar al'amuran tare da bada hadin kai ga masu ruwa da tsaki wajen tabbatar an ci karfin wannan cuta ta korona.