Coronavirus: Iyayen da ke fama da yara marasa ji lokacin kulle

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Joseph Lee
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A wurin wasu iyayen zama a gida tare da yaransu kanana na nufin fuskantar barazana da cin mutunci da takura ne za su karu.
Ya suke fama da wannan dokar ta hana fita da takaita zirga-zirga?
Julie ta gano cewa za ka iya sayen doguwar wuka a intanet, yayin da ta ga danta na caccaka wa kujerun gidanta wuka.
A 'yan watannin da suka gabata, sai da ta kira 'yan sanda sau biyu har gidanta, a baya-bayan nan an kulleta a bandaki yayin da danta wanda yake matashi ya yi kokarin karya kofar gidan da wuka don ya fita.
Yanzu duka iyalin na zaune tare a lokacin wannan dokar hana fita, suna fama da zaman kadaitaka, rashin hadin kai da zaman tsoro.


Ta ce ta yi amannar dan nata ya kira 'yan sanda ne ba da nufin cutar da ita ba, kawai dai don ya nuna mata bacin ran da yake ciki ne.
Amma sau biyu ko sau uku ya yi mata barazana cikin mako guda, in ji ta.
Liam ya yi fama da damuwa a matsayinsa na matashi ya kuma fada cikin matsalar kwakwalwa, kullum cikin yanayin tausayi.
Iyalan gidan da abokai da makwabta na kokari wajen tafiyar da fushinsa duk lokacin da irin wannan matsalar ta motsa domin tausasa fushin da yake fama da shi.
Amma wannan dabarar da suke yi masa wata barazana ce ga dokar nisantar juna.
Mijinta sai dai ya fita waje ya rika aiki, don haka duk lokacin da babu wadanda za su taimakawa Julie ta ce "Ina matukar shan wahala".
Ba dai a san takamaimai iyaye nawa ne ke rayuwa da fitinannun yaransu ba a cikin wannan yanayi.
Amma rahotannin irin wadannan matsaloli da BBC ta samu a bara sun nuna adadin ya ninka sau biyu daga wannan 14,133 wanda aka samu tsakanin 2015 da 2018 - ban da wadanda ba a shigar da kararsu ba.

Kamar rayuwa ne da fitinannen yaro
Helen Bonnick, wata tsohuwar ma'aikaciyar wayar da kai ce kan wannan batu, ta ce shaidu sun nuna cewa daya cikin 10 na iyaye na fama da matsalar hatsabiban yara, amma sauran abubuwan da ke faruwa ana samunsu sai dai ba akai-akai ba.
Wasu yaran masu matsanancin fushi kuma ana shan wuya da yadda ake iya shawo kan wannan halayyar tasu, amma ta ce wasu kuma na yi ne da gangan kuma za a iya shawo kan tasu matsalar, saboda ma fi yawa fitina ce ta balaga.
Wannan dokar hana fitar ta kara ta'azzara fitinar da ke cikin irin wadannan iyalai, tare da kara jaddada sakon da irin wadannan fitinannun yara ke aike wa ga iyayensu.
"Saboda ba sa iya fita suna zaune ne tare da iyayen wuri daya za su iya aikata abin da suke so ba tare da sanin kowa ba," in ji Misis Bonnick.
"Iyayen da ke fuskantar muzgunawa daga abokan zamansu da kuma fitinar 'ya'yansu na cewa abin ya fi kazanta a gurinsu - saboda jini da tsokarka ne," in ji ta.
Neils wanda ke zaune a gabashin Ingila ya ce, fushin dansa Ben abin sha'awa ne lokacin da yake shekara hudu, amma da ya kai shekara takwas sai abun ya munana.
Yanzu yaron ya "fara balaga ya kara zama cikakken mai hadari," ta yadda Ben yanzu yake iya daukar wukake ko kwalabe.
Ben ya zama kamar mai tabin hankali ga shi yana da wahalar koyon abubuwa da wuri.
Da zuwan wannan annoba ta korona ta jawo karuwar fitinarsa da kuma kara fusata shi ko da yaushe, kamar yadda mahaifinsa ya bayyana.
"Yana kaunar ya rika toye-toye ko dafe-dafe ko da yaushe, ba wani abu ba ne mai wuya a wurinsa yanzu ya birkice.
''Zama da shi kamar kana zaune da bam ne da zai iya tashi ko da yaushe" in ji Neil.
"Rayuwa na cikin kunci kuma korona ta kara kuntata ta," in ji Neil.
Peter Jakob, wani likita ne da yake taimakawa mutane da suke fuskantar irin wannan yanayi ya ce, killacewa da kunyar da iyaye ke fuskanta shi ne babban kalubalen da ke damunsu daga yaransu.
Ya ce amma za a iya shawo kan matsalar, ko da a wannan lokaci na hana fita.
Dakta Jakob ya ce kamata ya yi iyaye su samar da wani lokaci na abin da ya kira "nuna kulawa" - wanda ko bayan faruwar abin, mutane da dama za su rika mu'amala da yaran ta hanyar tura sakonni da kira ta bidiyo kamar ta manhajar WhatsApp ko FaceTime.
"Da yawan yaran ba sa son wasu su san suna da fitina ko tashin hankali ko kuma wani abu da kan iya jan rikici," ya ce.
Idan suka ga iyayensu na ci gaba da fadawa mutane halayyarsu, hakan zai iya tilasta musu sauyawa, ya kara da cewa.

Ka zama mai daukar mataki yana da amfani
Amma Suzzane Jacob, shugabar kungiyar da ke yaki da cin zarafin dan adam ta ce, iyayen da ke irin wannan yanayi na da bukatar fahimtar da hukumomi da al'umma.
Ta ce sau da yawa yaran na amfani da dokar hana fita wajen kalubalentar iyayensu, saboda sun san idan suka matsa musu za a ce sun karya doka.
"Yayin da iyaye ke fuskantar tuhuma kan abin da ba su aikata ba, suna fuskantar goyon baya da kuma yadda mutane ke kasa fahimtar halin da suke ciki," ta kara da cewa.
Misis Jacob ta ce tana son gwamnati ta yarda cewa gida ba wajen samun kwanciyar hankali ba ne ga wasu mutanen, ko dai iyayen da ke cutar da yaransu ko kuma iyayen da ke da fitinannun yara.
"Kawai su yarda akwai mutanen da ke bukatar taimako.
Masu hikima na cewa ka yarda da faruwar abu na nuna alamun daukar mataki wanda kuma ke da muhimmanci - wannan ya tabbatar da cewa abu ne da ke ci gaba," in ji ta.
''Wadannan sakonin za su taimakawa mutanen jin cewa babu abin da ya dame su.''














