Coronavirus: Kusan rabin wadanda suka kamu a Nijar sun warke

Asalin hoton, Getty Images
A Jamhuriyar Nijar kusan rabin mutanen da suka kamu da cutar korona sun warke inda tuni dukkansu suka koma gida.
Akalla mutum 671 ne suka kamu da cutar a kasar inda 391 har yanzu ke shan magani.
Mutum 256 ne dai aka tabbatar sun warke daga cutar ta korona inda 24 kuma suka mutu a kasar.
Annobar dai ta fi yaduwa a birnin Yamai inda masu wadanda suka kamu suka kai 628, sai kuma jihohin Tawa da Damagaram wadanda ke bin Yamai da mutum 12 kowacce jiha.
Jihar Dosso kuwa na da mutum 11, sai Tilabery 5, sai kuma jihar Maradi wadda aka gano mutum uku masu dauke da cutar yanzu an tabbatar sun warke.
Ba a samu bullar cutar korona a jihohin Agadez da Diffa ba kawo yanzu.

Matashiya
A ranar 19 ga watan Maris din daya gabata ne aka samu bullar cutar korona a kasar ta Nijar inda wani dan kasar Italiya ya shiga da ita.
Tun daga wannan lokacin ne gwamnatin kasar ta dauki matakai daban-daban na kariya don dakile yaduwar cutar.
Daga cikin matakan hana jam'in sallah a masallatai da kuma dokar takaita zirga-zirga a birnin Yamai ne suka haifar da fito na fito a tsakanin wasu mazauna unguwanni birnin da kuma jami'an tsaro.
Dauki ba dakin da aka yi da wasu mazauna birnin da jami'an tsaron ya sa an kama mutum 808.
Tuni dai gwamnatin kasar ta sassauta dokar takaita zirga-zirgar inda aka mayar da lokutan fita daga karfe 9 na dare zuwa 5 na asuba.












