Coronavirus: An tilasta rufe baki da hanci a Nijar

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin birnin Yamai a Nijar sun tilasta wa mutane amfani da abin rufe baki da hanci a fuska a matsayin kariya ga cutar coronavirus.
Tuni Majalisar dokokin Nijar ta amince da sanya dokar ta-baci tsawon wata uku a fadin kasar.
Wakiliyar BBC a Yamai ta ce dokar rufe baki da hanci ta shafi mutanen birnin Yamai inda cutar ta fi bazuwa, kuma tun a ranar Asabar ta fara aiki, yayin da kuma dokar ta-baci da majalisa ta amince za ta fara aiki daga ranar Lahadi har zuwa 11 ga watan Yuli.
An shawarci mutane su dinga rufe baki da hanci ko da rawani ko hijabi musamman a kasuwa da tashar mota a matsayin kariya.


Tun bullar cutar a watan Maris Hukumar koli ta addinin Musulunci a Nijar ta sanar da soke tarukan sallar juma'a da sauran sallolin jam'i domin dakile bazuwarta a kasar.
A lokacin kiran sallah, ladan yakan yi kira ga al'umma su yi sallah a gida maimakon fitowa masallaci.
Zuwa yanzu hukumomi sun ce akwai mutum 430 a Nijar da ke fama da cutar coronavirus, a cikinsu hamsin sun warke, yayin da 11 kuma suka rasu.







