Me ya jawo karuwar mace-mace a Kano lokacin da ake fama da annobar Covid-19?

Kano

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyoyin al'umma sun fara neman ba'asi daga bangaren gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya kan yawan mace-macen da ake samu a jihar Kano da ke arewacin kasar musamman a 'yan kwanakin nan bayan da aka fara samun bullar cutar korona a jihar.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na fararen hular na yin wannan kira ne ga gwamnatin Kano bisa damuwar da jama'a ke kara nunawa kan yawan mace-macen da ake samu fiye da abin da aka saba gani.

A kwanakin karshen makon nan ne dai wasu daga cikin al'ummar jihar suka fara nuna damuwarsu dangane da yadda ake samun yawaitar mace-mace, inda ake binne mutane da dama a makabartu daban-daban da ke fadin birnin Kano.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa ana samun karuwar mace-mace.

Bala Abdullahi Gabduwama shi ne shugaban gamayyar kungiyar kare hakkin dan adam ta Nerwork For Justice da ke Kano, ya ce a kullum a kan samu karin yawan mace-mace na al'ummar jihar, inda ya ce akwai ayoyin tambaya da ya kamata a dasa, musamman yadda al'umma ke ci gaba da nuna damuwa.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Alkaluma mabambanta ne dai ake samu na mutanen da ake binnewa a makabartun jihar daban-daban.

Wakilin BBC da ya ziyarci Makabartar Dandolo da safiyar ranar Litinin ya ce ya hangi rukunin mutum uku da zo daga unguwanni daban-daban da suka kai gawarwaki don binnewa.

Daya daga cikin masu kula da makabartar da ya nemi a boye sunansa ya ce tun daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa safiyar Litinin an binne kusan mutane 50 a makabartar Dan Dolo.

Ya ce rabon su da su sami irin hakan tun lokacin da Boko Haram ta kai hari babban Masallacin Juma'a da ke Kano a shekarar 2014.

''A ranar Juma'a a lissafin nan bangarenmu mun binne 12, a ranar Asabar mun yi 11 a ranar Lahadi mun yi guda takwas, yanzu kuma a ranar Litinin da safe mun binne 10. Ni dai rabon da na ga haka tun harin Masallacin Juma'a na Gidan Sarki,'' in ji shi.

A makabartar Gidan Gona da aka fi sani da Makabartar Tarauni, wasu daga cikin masu kula da makabartar ya shaida wa BBC cewa tun kwanaki biyar da suka gabata yawan wadanda ake binnewa a makabartar ya karu.

Ya kara da cewa a safiyar Litinin kadai iya mutum hudu ne aka binne a makabartar, amma jumullar adadin wadanda aka kai makabartar sun kai kusan 55, sannan kusan mafi yawancin lokutan zafi da farkon kowane azumi sukan sami yawan gawarwakin da akan binne amma ba su kai na wannan shekarar ba.

Bala Abdullahi Gabduwama ya ce: ''Gaskiyar magana a yanzu za mu ce muna cikin wani yanayi na ana shan maganin kaba amma kai yana kara kumbura. Ga shi dai an killace mutane a gidajensu.

''Muna bai wa gwamnati shawara da ta fara lekawa lungu-lungu tana zakulo wadanda watakila suke dauke da cutar nan, da kuma wadanda ke cikin yanayi na rashin lafiya a gidajensu.''

Karin labaran da za ku so ku karanta

Dalilan mace-macen

Farfesa Isa Sadik Abubakar, shugaban sashin cututtuka masu yaduwa na Jami'ar Bayero da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce a fahimtarsu watakila yawan mace-macen ba ya fi na da ba ne.

Saboda "Idan asibitoci ba sa cikin hayyacinsu ba sa bayar da taimako yadda aka saba, babu mamaki irin wadannan mutanen su shiga wani hali na shan wuya watakila ma a samu wasu daga cikinsu su rasu," in ji Farfesan.

Wasu masana harkar lafiyar kuma na ganin cewa tsoron da marasa lafiya ke yi na zuwa asibiti a lokacin wannan annoba ya sa da dama masu fama da wasu cututtukan masu tsanani ba sa son zuwa asibiti, lamarin da ke jawo musu rashin samun kulawa da taimakon da suke bukata.

Sannan ga yanayi na zafi da dama an saba samun cututtuka daban-daban lokacinsa, da suke zama ajalin mutane.

Gwamnati ta musanta

Ita ma gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa ana samun karuwar mace-mace.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, Ma'aikatar Lafiya a jihar ta ce bincikenta ya gano babu alamar gaskiya a rahotannin da ake bayarwa.

Sanarwa ta kara da cewa kwamitin yaki da cutar korona a jihar yana sa ido kan mace-macen da ake yi, kuma ya tura jami'ai makabartu domin sanya ido da ba da rahoto kan adadin mutanen da ake binnewa.

To sai dai wasu na ganin mai yiwuwa hukumomi sun bayyana hakan ne kasancewar mafi yawan wadanda suke mutuwa ba asibiti suke zuwa ba, kasancewar mutane na tsoron zuwa asibiti a wannan yanayi na annobar korona, kuma su kansu asibitocin suna dari-dari da karbar marasa lafiya in dai ba wadanda ke bukatar kulawar gaggawa ba.