Gwamnati ta nemi afuwa kan jana'izar Abba Kyari

Jana'izar Abba Kyari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Hukumar birnin Abuja ta ce ta tsare ma'aikatan da ba su yi aikin yadda ya kamata ba yayin jana'izar

Shugaban kwamitin yaki da cutar korona a Najeriya, Mista Boss Mustapha, ya nemi afuwa saboda saba ka'idojin da aka yi wurin binne marigayi Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari a ranar Asabar.

Mista Mustapha ya ce abin takaici ne yadda ba a bayar da tazara ba a wajen jana'izar.

Ya nemi afuwar ne a lokacin da kwamitinsa ke bayar da bayanai kan ayyukan da suke yi wajen kawar da korona a Najeriya, yayin wani taron manema labarai na kullum da suke yi a Abuja.

Mutane da dama ne suka halarci jana'izar marigayi Abba Kyari a ranar Asabar, wanda ya rasu sakamakon cutar korona ranar Juma'a a Jihar Legas.

Yadda aka yi cincirindo ya sa mutane da dama suka soki jami'an gwamnati da suka ki bin dokar ba da tazara da aka kafa domin rage yaduwar cutar korona a Najeriya.

Shugaba Buhari ya gode wa wadanda suka taya shi alhinin rasuwar ta hanyar kiran waya da turo sakonni sannan ya yaba musu bisa bin umarnin guje wa tarukan zaman karbar gaisuwa.

Hana Jami'ai Shiga Villa

Bayan kammala jana'izar ne Fadar Shugaba Buhari ta haramta wa jami'an da suka halarci binne Malam Abba Kyari, inda aka bukace su da su killace kansu na kwana 14 kafin su shiga Aso Rock.

Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce "ba wani abin mamaki ba ne" don an hana su shiga Fadar Shugaban Kasa ta Aso Villa saboda sun halarci jana'izar Abba Kyari.

Isa Ali Pantami

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Ministoci da dama sun halarci jana'izar Abba Kyari

Mallam Garba Shehu yana mayar da martani ne kan rahotannin da ke cewa an rufe wa wadanda suka halarci jana'izar kofar shiga Villa.

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar har da Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami da shi Garba Shehu da kuma da yawa daga cikin mataimaka na musamman ga Shugaba Buhari a fannoni daban-daban.

"Ai da ma a mafi yawan lokacin nan ta intanet aka fi yin harkoki a Villa saboda haka ba wani sabon abu ba ne don an hana mu shiga," in ji Garba Shehu, a wani sako da ya wallafa a Twitter.

Ya kara da cewa: "An yi hakan ne bisa umarnin hukumar NCDC da kuma Ma'aikatar Lafiya. Ana yin hakan ne kuma domin dakile yaduwar cutar korona."

Tuni hukumar birnin Abuja ta FCTA ta ce an tafka kuskure yayin jana'izar ta Abba Kyari bayan an ga wani mutum yana jefar da kayayyakin kariyar da suka yi amfani da su a gefen titi bayan binne gawar a Makabartar Gudu.

Hukumar ta ce ta tsare ma'aikatan da ta gano ba su yi aikin yadda ya kamata ba domin ganin ko sun kamu da cutar da kuma dakile ta.

Isa Ali Pantami

Asalin hoton, Channels TV

Bayanan hoto, Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami yayi wa'azi wajen jana'izar