Coronavirus: 'Yan damfara na aika sakonnin email miliyan 18 kullum

A smartphone showing the Gmail logo

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Joe Tidy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Cyber-security reporter

'Yan damfara na aika sakonnin email miliyan 18 kowace rana kan cutar korona, ga masu amfani da Gmail, a cewar kamfanin Google.

Kamfanin fasahar ya ce annobar ta janyo karuwar damfara ta intanet sosai inda 'yan damfarar ke dabarar samun bayanai masu muhimmanci daga wurin mutane.

Kamfanin ya ce yana rufe adireshin email miliyan 100 kowace rana wadanda ake amfani da su wajen damfara.

A makon da ya gabata, kusan kashi daya cikin biyar na sakonnin email da aka tura na damfara ne da suka danganci cutar korona.

A iya cewa cutar a yanzu ita ce jigon damfara mafi girma, in ji kamfanin.

Mutum biliyan 1.5 ne ke amfani da adireshin email na Google wato Gmail.

Ana aika wa mutane dumbin sakonnin email kala-kala da ke nuna kamar daga hukumomi suke, akamr hukumar lafiya ta Duniya (WHO), a wani yunkuri na jan ra'ayin mutane su sauke wata manhaja ko kuma su bayar da gudumowa ga wani shiri na karya.

Haka kuma, 'Yan damfarar intanet na dogara da tallafin da gwamnati ke bayarwa ta hanyar kwaikwayon hukumomin gwamnatin.

Google ya ce manhajojinsa na toshe sama da kasha 99.9 cikin 100 na sakonnin email kafin su kai ga masu amfani da gmail.

A scam email impersonating the WHO. It encourages the recipient to "donate" money via Bitcoin.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Daya daga cikin sakonnin imail na karyar ya kwaikwayi Hukumar Lafiya Ta WHO

Kamfanonin tsaro na intanet da yawa na duba karuwar damfara ta hanyar amfani da cutar korona.

Kamfanin Barracuda Networks ya ce ya ga karuwar kashi 667 cikin 100 na sakonnin damfara na email a lokacin annobar nan.

'Yan damfara sun yi ta aika sakonnin email na karya da sakonnin waya inda suke nuna cewa daga gwamnatin Amurka da WHO da Hukumar yaki da yaduwar cutuka da ma wasu manyan jami'an Amurka ciki har da Shugaba Trump.

"Sakonnin email na damfara na da wani abu guda, dukansu na nuna tunzurawa ko kuma ya danganta da yanayin da ake ciki, don haka sakonnin ba za su ba mutum damar ya yi tunani mai zurfi ba a wannan lokaci ba," in ji mai bincike mai zaman kansa kan harkokin tsaro na intanet, Scott Helme.

"Annobar korona ta mamaye duka tunaninmu a halin yanzu kuma 'yan damfara a intanet sun fusknaci haka. Suna fatan mutane za su fi latsa bayanan da suka shafi cutar."

Another coronavirus scam email
Bayanan hoto, An aikawa wani kamfani wannan sakon imail din

'Son Zuciya'

Masu bincike sun gano shafukan intanet na damfara da manhajojin wayoyin zamani da ke dauke da bayanai na ainihi kan cutar korona.

Wata manhaja a wayoyin Android ta ce tana taimakawa wajen bindiddigin yaduwar cutar, amma maimakon haka, manhajar na lalata wayoyi da cutukan waya na ransomware sannan ta bukaci kudi kafin a gyara wayar ko kuma a cire ransomeware din.

A makon da ya wuce, Cibiyar Kula da Tsaron Intanet ta Burtaniya, NCSC da Ma'aikatar Tsaron Amurka sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa.

Sun ce sun ga "karuwar 'yan damfara a intanet" da ke "amfani da annobar Covid-19 don son zuciyarsu".

NCSC ta wallafa shawarwari a shafinta na intanet don taimakawa mutane su gane damfara a intanet.