Coronavirus: An bai wa marasa lafiya damar magana da danginsu ta waya

Dr Joel Meyer and Prof Louise Rose

Asalin hoton, Life Lines

Bayanan hoto, Wata kwararriyar ma'aikaciyar jinya Farfesa Louise Rose da wani babban likita Dr Joel Meyer ne suka fitar da wannan sabon tsari
    • Marubuci, Daga Jane Wakefield
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Fasaha

Asibitoci suna sassauta dokar da suka sa ta hana masu fama da coronavirus amfani da wayoyinsu yayin da suke dakin kulawa ta musamman wato ICU, a asibiti.

Ana hana masu fama da coronavirus ganin baki, ko da makusantansu ne.

Wata kungiyar agaji tana son ta samar da kwamfutocin hannu masu karfin intanet na 4G ga kowane dakin kulawar musamman da ke asibitocin Burtaniya, yayin da wasu ICU din kuma tuni suka fara bai wa marasa lafiyr damar amfani da wayoyinsu.

Wannan mataki ka iya taimaka wa wajen rage radadin kewar da suek fama da ita - ga wasu kuma, za su samu damar yin bankwana da iyalansu.

Sakataren ma'aikatar lafiya Matt Hancock ya sanar da cewa gwamnati tana tsara wasu dokoki ga iyalai don ba su damar ganawa da danginsu kafin su mutu.

Wata kwararriyar ma'aikaciyar jinya Farfesa Louise Rose da wani babban likita Dr Joel Meyer ne suka fitar da wannan sabon tsari.

Dr Meye ya ce ''Domin rage barazanar yaduwar cutar, a yanzu asibitoci na hana masu zuwa dubiya, abin da ke nufin cewa marasa lafiya ba za su dinga ganawa da iyalansu ba da zarar an kai su ICU.''

"Rashin ganawa da 'yan uwa a wannan lokaci na annoba babban tashin hankali ne.

''Duk da cewa ana sanya marasa lafiya bacci, jin muryar wani makusancinka na iya kwantar maka da hankali.''

Ba a barin likitoci da ma'aikatan jinya su shiga ICU da wayoyinsu saboda barazanar yada cutar.

Sign saying no visitors allowed outside hospital

Asalin hoton, Getty Images