Coronavirus: Yadda cutar ta bulla Jihar Kano

Asalin hoton, Getty Images
Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta zama ta baya-baya nan da cutar Coronvirus ta bulla a kasar.
A ranar Asabar ne hukumomi suka sanar da manema labarai cewar wni mutum ya kasance na farko wanda ya kamu da cutar a jihar.
Bayanan da hukumomi suka fitar sun nuna cewa mutumin, wanda yake zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajibirin ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.
Mai bai wa Gwamna Ganduje shawara kan harkokin sada zumunta Salihu Tanko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yanzu haka ana dakon sakamakon gwajin da aka yi wa makunsantan shi mutumin.


Bayanai sun nuna cewar yanzu haka an killace mutumin a cibiyar killace mutane da ke Kwanar Dawaki.
A Jawabinsa na musamman ga al'ummar jihar kan bullar cutar coronavirus a Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce za a dauki tsauraran matakai domin kare al'umman jihar.
Daga cikin matakan, Gwamnan ya haramta wa A daidaita sahu daukar mutum fiye da daya.
Dama tuni aka samu bullar cutar a jihohin da ke makwabtaka da Kano, wato Kaduna da Katsina.
A Kaduna mutum shida ne aka sanar suna dauke da cutar zuwa yanzu, yayin da a Katsina kuma an tabatar da mutum hudu da suka kamu har ma daya daga cikinsu ya rasu tuni.
Jihar Kano ta zama ta 19 daga cikin 36 da cutar ta bulla a Najeriya bayan jihohin Neja da Anambra da suka sanar da bullar cutar a ranar Juma'a.
Hukumar da ke dakile cututtuka masu yaduwa NCDC zuwa Juma'a da yamma ta tabbatar da cewa mutum 305 ne suka kamu da cutar a fadin kasar.

Karin labaran da za ku so ku karanta












