Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari 'bai yi wa arewacin Najeriya adalci kan cibiyoyin gwajin Coronavirus ba'
Wasu al'umma a arewacin Najeriya na nuna damuwa game da yadda ake da cibiyoyin binciken cutar coronavirus har biyar a yankin kudancin kasar amma babu ko daya a arewaci.
Masu wannan korafin dai na ganin ba a yi wa al'ummar yankin adalci ba, kamar yadda Malam Abdulrahman Kwacam, shugaban matasa na arewa maso gabashin Najeriyar ya shaida wa BBC.
Malam Abdulrahman ya ce, " Wannan abu ne na takaici kuma na tashin hankali wanda ni a ganina shugaban kasa ba ya mana adalci mu a arewa".
Ya ce "Ba a san wadanda ke dauke da wannan cuta ba musamman a arewa ai ba a san da wadanda masu dauke da cutar suka yi hulda ba".
Shugaban matasan na arewa maso gabashin Najeriyar ya ce, " A kudanci akwai cibiyoyin gwajin wannan cuta guda hudu ko biyar, to wannan ya nuna karara cewa gwamnati bata damu da mutanen arewa ba".
Ya ce yakamata ya yi gwamnati ta tashi ta kai irin wadannan cibiyoyi inda babu cutar da inda ma akwai ta don a tantance su wa ke da cutar.
To sai dai kuma a nata bangaren gwamnati ta bakin mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin siyasa, Abdulrahman Baffa Yola, ya ce an samar da cibiyoyin ne a kudancin Najeriyar don dakile bazuwar cutar zuwa sauran sassan kasar.
Abdulrahman Baffa Yola, ya ce " Ina ganin akwai karancin fahimta ga mutanen da suke fadar irin wadannan maganganun, gwamnati babu ta inda ta nuna banbanci ko fifiko a bangarorin Najeriya".
Ya ce " A kan harkar yaki da cutar coronavirus ma babu ta inda gwamnatin ta yi wani abu da za a ce an nuna fifiko domin an kai wadannan cibiyoyin ne a wuraren da wannan cuta ta fara bazuwa don gudun ka da ta yadu a sauran jihohi".
Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin siyasar ya ci gaba da cewa, ba komai ne gwamnati zata yi sai ta fito ta sanar ba".
Ya ce a yanzu abin da yakamata ayi shi ne a ci gaba da wayar da kan mutane ta yadda za a kaucewa yaduwar wannan cuta maimakon a rinka zantuka irin wadannan.
To sai dai kuma a yayin da ake wannan turka-turka, cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Najeiriyar NCDC, ta wallafa a shafinta na twitter cewa zata kara samar da cibiyoyin binciken daga shida zuwa goma sha uku.
NCDC ta ce, za a samar da cibiyoyin ne a arewacin kasar in banda guda biyu da za a yi a Fatakwal da Abakaliki.
Za dai a samar da cibiyoyin gwajin cutar coronavirus din ne a garuruwan Sokoto da Kano da Maiduguri da Jos da kuma Kaduna.
Karin labaran da za ku so karanatawa: