Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
"Buhari bai yi wa Arewa adalci kan tallafin coronavirus ba"
Bayan da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da wasu karin matakai don hana bazuwar cutar koronabairus a sassan kasar ciki har da bai wa Legas ta kudu maso yammaci, inda annobar ta fi ta'azzara, tallafin naira biliyan 10, wasu 'yan arewa ke ta tsokaci tare da sukar shugaban.
Amma dai jam'iyyar APC ta Shugaba Buhari ta ce bai kamata a mayar da wannan al'amari na bala'i, siyasa ba.
Akasari dai suna zargin Shugaba Buhari ne da nuna bambanci ko fifita jihar Legas a kan sauran jihohin kasar musamman na arewacin Najeriya, duk da yake mutane kalilan ne cutar ta shafa a can zuwa yanzu.
Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya ta ce jihar Legas ya zuwa daren Juma'a, an tabbatar da samun mutum 52 da ke fama da cutar koronabairus.
Ana kuma fargabar cewa wannan adadi na iya karuwa, daidai lokacin da hukumomi suke ci gaba da bin sawun mutanen da ake jin sun yi hulda da masu dauke da kwayar cutar.
Sai dai wasu da dama ciki har da 'yan jam'iyyar APC ta Shugaba Buhari na da ra'ayin cewa matakin da jagoran ke dauka na nuna tamkar ya fi fifita kudancin kasar ne a kan arewaci.
Wani rikakken dan jam'iyyar APC daga jihar Kano, Malam Anas Abba Dala ya ce a ganinsa, shugaban bai yi adalci ba saboda "ya nuna gaba daya 'yan arewacin Najeriya ba ya kaunarmu, kuma zargin da muka dade muna yi ya tabbata."
Abba Anas ya ce "kowacce kasa idan ka je, wajen da al'umma suka fi yawa, nan gwamnati take zuwa ta yi kokarin magance irin wannan cutar."
Ya bayyana takaicinsa kan yadda shugaban kasar ya amince da ware naira biliyan 15 domin yaki da cutar kuma daga cikin adadin aka bai wa gwamnatin Legas naira biliyan 10 ba tare da bai wa yankin arewa ko anini ba.
A cewarsa, "Mu ne 'yan uwansa da muka fi kowa ba shi kuri'u amma yau gaba daya yankin arewa bai ba wa kowa komai ba, don haka wannan ba adalci ba ne".
Malam Abba Anas ya ce ai jihar Legas ba ita kadai ba ce a Najeriya.
Sai dai da yake martani kan ikirarin dan jam'iyyar APCn, babban jami'in walwala na kasa a jam'iyyar mai mulki, Alhaji Ibrahim Masari ya ce bai kamata a sanya siyasa cikin lamarin ba.
Ya ce bai kamata wata jiha ta yi fatan samun irin kudin tallafin na yaki da annoba ba saboda a ganinsa, "komai akan mayar da shi siyasa. Na dauka maganar lafiya daban, maganar siyasa ma daban,"
"Wane ne yake fatan ya karbi irin wannan kudi na iftila'i? Ya ce idan dala biliyan daya za a bayar tallafi, kamata ya yi mutum ya yi fata kada ma abin ya zo gare ka, a ba wasu," in ji Ibrahim Masari.
Ya ce annobar koronabairus ba ta yi kamari a arewacin kasar ba saboda cutar ta fara ne daga Legas kuma nan ne aka fi samun yawan masu fama da cutar a Najeriya.
"Kada a siyasantar da wannan musiba da ta addabi duniya baki daya ba ma Najeriya ba." kamar yadda babban jami'in walwalar na jam'iyyar ta APC ya fada.
Da ma ba tun yau ba ne ake samun wasu 'yan kasar suna zargin shugaba Buhari da mayar da yankin arewacin kasar bora sai dai gwamnatin ta sha bayyana cewa tana kamanta adalci kuma babu wata jiha 'yar mowa a wajenta.