An zargi Koriya ta Arewa da harba makamai masu linzami

Lokacin karatu: Minti 2

Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta harba wasu abubuwan fashewa biyu zuwa teku wadanda ta ce sun yi kama da makamai masu linzami.

An harba makaman ne daga Lardin Pyongan ranar Asabar zuwa tekun Japan.

Amurka da China sun nemi a koma teburin tattaunawa kan maganar kawo karshen shirin nukiliya da kawo karshen kera makamai masu linzami.

A ranar asabar ne rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce tana bibiyar lamarin ko da za a samu karin wasu makaman da za a harba.

Japan ta tabbatar da dirar makami mai linzami a wajen ruwan da ke yankin tattalin arzikinta na musamman.

Lamarin na zuwa ne yayin da Koriya ta Arewa ta sanar da gudanar da wani babban taro da majalisar kasar ranar 10 ga watan Afrilu.

Sai dai masu sharhi sun ce taron zai hada manyan jagororin kasar su 700 a waje guda.

Wata ma'abociyar dandalin sada zumunta na Twitter Rachel Minyoung ta ce taron zai kasance dama ga Koriya ta Arewa ta ba da tabbaci game da kokarin da take na magance coronavirus.

Kawo yanzu dai ba a samu bullar coronavirus a Koriya ta Arewa ba amma wasu kwararru na bayyana kokwanto.

Koriya ta Arewa na da iyaka da China inda cutar ta samo asali da kuma Koriya ta Kudu inda aka samu barkewar cutar sosai.

Wani babban jami'in sojin Amurka a makon da ya gabata ya ce yana da "tabbaci" cewa cutar ba ta bulla a Koriya ta Arewa ba.

Kasar dai ta killace kusan baki 380 - mafi yawansu jakadu da ma'aikata a Pyongyang - a harabar gidajensu na kusan wata daya.

An kuma dage takunkuman da aka kakaba a farkon watan nan na Maris.