Amurka na fatan dage haramcin biza a kan 'yan Najeriya

Amurika ta ce za ta duba yiwuwar janye haramcin wani rukuni na biza da ta yi wa 'yan Najeriya na shiga kasarta.

Yayin wani taron manema labarai tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ministan harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyema, Mista Pompeo ya ce Amurka ta dauki matakin ne saboda karuwar aiyukan ta'addanci a kasashen yammacin Afrika ciki har da Najeriya.

Dalilin da aka bayar shi ne Najeriya da wasu kasashe biyar da abin ya shafa ba su cika ka'idojin tsaro da kuma bayar da hadin kai wurin magance tafiye-tafiye tsakanin kasashe ba bisa ka'ida.

Sai dai wata sanarwa da aka fitar bayan ganawar, ta ambato sakataren harkokin wajen Amurkan na cewa ''muna fatan janye wannan haramci kuma za mu duba yiwuwar hakan''.

Yayin ganawar ministan harkokin wajen Najeriyar ya ce tuni kasar ta fara duba yadda za ta shawo kan matsalolin da Amurkan ta yi nuni da su.

A shekarar 2018, Amurka ta bai wa 'yan Najeriya takardun izinin shiga kasar ninki biyu fiye da jumillar wadda ta bai wa sauran kasashen biyar.

Wani jami'i ya ce an dauki sabbin matakan ne saboda gazawar kasashen shida ta cimma ka'idar Amurka ta musayar bayanan tsaro.

Mene ne haramcin?

A shekarar 2017 Trump ya sanya hannu kan dokar nan ta haramta shiga Amurka da ta janyo ce-ce ku-ce, kwana bakwai bayan zamansa shugaban Amurka a watan Junairu, inda ya ce "tana da muhimmacin wajen kare Amurkawa".

Da farko haramcin ya shafi kasashe bakwai ne da ke da rinjayen Musulmi, sai dai an yi wa kasashen kwaskwarima sakamakon kalubalantar matakin a kotuna daban-daban.

A yanzu haramcin ya shafi 'yan kasashen Iran, da Libya da Somalia da Syria da Yamen da Venezuela da Koriya ta Arewa.

Yayin da gwamnati ta dakatar da ba da takardar izinin shiga kasar ga mafi yawan 'yan cirani, da ma wasu masu neman izinin shiga kasar, ana sa ran cewa dalibai da mutanen da suke da alaka da Amurka za su ci gaba da samun damar shiga kasar.