Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Donald Trump zai hana masu zuwa Amurka haihuwa shiga kasar
Amurka ta ce daga yanzu ba za ta kara bai wa baki 'yan kasashen waje da ke zuwa haihuwa kasar izinin shiga kasar ba.
A wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar cikin gida ta kasar, ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a 24 ga watan Janairu.
Hakan na nufin matan da ke neman izinin shiga kasar a matsayin bakunta sai sun nuna wata hujja mai karfi ta son zuwa Amurkan maimakon son haihuwa a can.
Matan Najeriya da dama sun mayar da Amurka wajen zuwa haihuwa domin samar wa 'ya'yansu takardun zama 'yan kasa.
Wannan lamari dai ya fara janyo muhawara sosai a shafukn sada zumuntar Najeriya