Trump ya hana 'yan ci rani daga Najeria da kasashe biyar shiga Amurka

Amurka ta sanar da fadada haramcin ba da takardun izinin shiga kasar, wato biza, inda ta kara kasashe shida ciki kuwa har da Najeriya, kasa mafi yawan mutane a nahiyar Afirka.

Daga yanzu za a hana 'yan kasashen Najeriya da Eritrea da Sudan da Tanzania da Kyrgyzstan da Myanmar samun wani rukuni na bizar.

Amma 'yan kasar za su iya shiga Amurkar a matsayin masu yawon bude ido da shakatawa.

A shekarar 2018, Amurka ta ba wa 'yan Najeriya takardun izinin shiga kasar ninki biyu fiye da jimillar wadda ta bai wa sauran kasashen biyar.

Wani jami'i ya ce an dauki sabbin matakan ne saboda gazawar kasashen shida ta cimma ka'idar Amurka ta musayar bayanai na tsaro.

"Kasashen suna so su ba da hadin kai a mafi yawan bangarori, amma saboda da wasu dalilai, sun kasa cika sharudan da muka gindaya musu," a cewar mukaddashin sakataren tsaron cikin gida Chad Wolf a hirarsa da 'yan jarida ranar Juma'a.

Yace hukumomi suna aiki da kasashen dan karfafa tsarinsu na tsaro domin taimaka musu wajen ganin an cire su daga kasashen da aka sanya wa haramcin.

A shekarar 2017 ne Shugaban Amurka Donald Trump ya fara sanya harmacin shiga Amurka. A yanzu haka ta rufe iyakokinta ga kasashen bakwai, da mafi yawan 'yan kasashen suke musulmi.

A shekarar 2018 Amurka ta baiwa fiye da 'yan ci rani 8,000 daga Najeriya izinin shiga Amurka. A shekarar kuma an ba wa 'yan Sudan 2,000 bizar shiga Amurkar, mutum 290 daga Tanzaniya sannan aka ba wa 'yan Eriterea 31 kawai.

Dama Amurkar ta bayyana haramcin ba da wasu rukunin biza ga 'yan Eriterea a 2017.

Me sabon haramcin ya kunsa?

Amurka ta ce za ta dakatar da ba da biza da za ta bai wa mutum damar zama dan Amurka ga 'yan Najeriya, da Eritrea da Kyrgyzstan da Myanmar.

'Yan Sudan da 'yan Tanzania ba za su samu damar neman shiga Amurka ba rukunin "diversity visas", wacce 'yan wasu kasashe ke iya samu ta hanyar caca.

Mr Wolf ya ce, 'yan kasashen za su iya neman bizar takaitaccen zama - da suka hadar da ta masu ziyara, da ta masu yin kasuwanci, ko kuma mutanen da suke neman magani, duka wadannan mutanen haramcin bai shafe su ba.

Daga cikin kasashen da suke fuskantar sabon haramcin, Najeriya ce ta fi yawan 'yan ci rani dake zuwa Amurka.

Alkaluman gwamnatin na Amurka sun nuna cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bai wa 'yan ci rani daga Najeriya 8,018 biza a 2018.

Mafi yawan 'yan Kyrgyzstan da Sudan musulmi ne, yayin da kimanin 50% na 'yan Najeriya da Eritrea suke Musulmi. Ita ma Tanzania tana da Musulmi da dama.

Menen haramcin?

A shekarar 2017 Trump ya sanya hannu kan dokar nan ta haramta shiga Amurka da ta janyo ce-ce ku-ce, lwanaki bakwai bayan zamansa shugaban Amurka a watan Junairu, inda ya ce tana da muhimmacin wajen kare Amurkawa,

Da farko haramcin ya shafi kasashe bakwai ne dake da rinjayen musulmi, sai dai an yi wa kasashen kwaskwarima sakamakon kalubalantar matakin a kotuna daban daban.

A yanzu haramcin ya shafi 'yan kasashen Iran, da Libya da Somalia da Syria da Yamen da Venezuela da Koriya ta Arewa.

Yayin da gwamnati ta dakatar da ba da takardar izinin shiga kasar ga mafi yawan 'yan ci rani, da ma wasu masu neman izinin shiga kasar, ana sa ran cewa dalibai da mutanen da suke da alaka da Amurka za su ci gab da samun damar shiga kasar.