Coronavirus ta zama annoba ta duniya – WHO

Yawan wadanda suka kamu da cutar a wajen China ya ninka har sau 13 cikin mako biyu da suka gabata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawan wadanda suka kamu da cutar a wajen China ya ninka har sau 13 cikin mako biyu da suka gabata

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce cutar numfashi ta oronavirus ta zama annoba ta duniya.

Shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yawan wadanda suka kamu da cutar a wajen China ya ninka har sau 13 cikin mako biyu da suka gabata.

Ya kuma ce ya "kadu sosai" da "yanayin yadda aka gaza" dakile cutar.

Annoba ta duniya, ita ce cutar da ta karwade duniya a lokaci guda - ana kiranta world pandemic da Ingilishi.

Sai dai Dr Tedros ya ce bayyana cutar da annoba ta duniya da aka yi ba ya nufin cewa WHO ta sauya shawarar da take bai wa kasashe kan yadda za su tunkare ta.

Ya yi kira ga gwamnatoci da su sauya matakan da suke dauka da "gaggawa da kuma ba sani ba sabo".

"Kasashe da dama sun nuna cewa za a iya dakile wannan cuta," in ji shi.

"Kalubalen da kasashe masu fama da dumbin jama'ar da ke dauke da kwayar cutar ba wai shi ne cewa ko za su iya ba - maganar ita ce ko za su yi hakan.

"Muna tare a wannan yakin domin yin abin da ya dace cikin natsuwa da niyyar kare jama'ar duniya. Za a iya."