Premier League: An dage wasan Arsenal da City saboda coronavirus

Asalin hoton, Getty Images
An daga wasan Premier da Manchester City za ta buga da Arsenal ranar Laraba a wani matakin kariya daga yaduwar cutar coronavirus.
Da yawa daga cikin 'yan wasan Arsenal sun killace kansu a gida bayan sun yi mu'amala da mai kungiyar Olympiakos Evangelos Marinakis.
Arsenal ta ce Marinakis mai shekara 52, ya hadu da wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar lokacin da Gunners din ta karbi bakuncin kungiyar Girka a wasan Europa mako biyu da suka gabata.
A ranar Talata, Marinakis wanda shi ne mamallakin kungiyar Notteingham Forest, ya ce an gwada shi kuma ba ya dauke da cutar ta Covid-19.
Yanzu dai Olympiakos za ta karbi bakuncin Wolves ranar Alhamis a wasansu na Europa.
Uefa ta ki amincewa da bukatar Wolves ta a daga wasan saboda tsoron coronavirus.
Hukumar Premier ta ce ana daukar duk wasu matakai da suka dace na kariya.
Brighton ta ce wasanta da Arsenal ranar Asabar za a yi shi ne babu 'yan kallo.
Rahotanni na cewa ya zuwa yanzu akwai mutum 382 da suka kamu da cutar a Burtaniya, kuma tuni wasu shida suka mutu.











