Atlanta ta kora Valencia gida da kwallaye masu yawa

Asalin hoton, Getty Images
Atlanta ta tsallaka zagayen kusa da daf da nakarshe na gasar zakarun turai, bayan cinye Valencia da ta yi da ci 3-4.
Dama Atlanta ta zo da nasarar da ta samu a Italiya ta kwallo 4-1.
Tun aminti uku da fara wasan Atlanta ta samu bugun finareti inda Josip Ilicic ya buga kuma ya ci.
A minti na 21 ne dan wasan gaban Valencia Kevin Gameiro ya farke wannan kwallo, abin da ya baiwa kungiyar kwarin gwiwar neman kara kwallo.
Kwallon da Mouctar Diakhaby ya taba da hannu ita ce ta kara bai wa Josip Ilicic damar kara zira kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 43.
Kevin Gameiro ne ya kara farkewa wasa ya dawo 2-2, Ferran Torres ya kara wa Valencia kwallo a ragar Atlanta a minti na 67 aka yi 3-2.
A minti na 71 da na 82 Josip Ilicic ya kara kwallo biyu wasa ya koma 3-4, kuma a haka aka tashi.
Josip Ilicic shi kadai ya ci kwallo hudu cikin takwas da aka ci Valencia gida da waje.
An dai buga wasan ne ba tare da magoya baya ba, saboda gujewa cutar nunfashi ta coronavirus.











