RB Leipzig ta yi waje da Tottenham daga Champions lig

Asalin hoton, Getty Images
RasenBallsport Leipzig ta zazzaga wa Tottenham kwallo 3-0 a raga, ta kuma koreta daga gasar Champions.
Tun a minti na 10 da fara wasan ne Marcel Sabitzer wanda shi ne kyaftin din kungiyar ya fara zira kwallo ta farko.
Minti 11 tsakani ya kara samun wata kwallon da aka kwaso masa ya sa mata kai ta shiga raga, sai dai mai tsaron ragar Tottenham Lloris yayi maza ya ciro ta, amma alkalin wasa ya bayar da ci.
A na daf da tashi daga wasan ne Emil Forsberg ya kara kwallo ta uku a dai-dai minti na 87.
Tun a wasan farko da aka buga a gidan Tottenham an zira mata kwallo daya, idon aka hada da wadannan uku an zira mata kwallo hudu kenan gida da waje.
Matsalar rauni na daga cikin abubuwan da suka jawo wa Tottenham da kocinta Mourinho koma baya a gasar.
A yanzu dai haka cikin 'yan wasanta da ke fama da rauni akwai Harry Kane da Son Heung-min da Steven Bergwijn da kuma Moussa Sissoko.







