Ministar Lafiyar Birtaniya ta kamu da cutar Coronavirus

Ministar Lafiyar Birtaniya, Nadine Dorries ta kamu da cutar Coronavirus, ita ce 'yar majalisar dokokin kasar ta farko da ta kamu da cutar.
Ministar ta sanar cewa a yanzu ta killace kanta a gida, yayin da hukumomi ke ta kokarin gano inda ta kwaso cutar.
Ko a ranar Alhamis ta halarci wani taron cin abinci da Fira minista Boris Johnson ya shirya a fadar gwamnati da ke titin Downing.
Kusan mutun 400 ne cutar coronavirus ta kama a Birtaniya inda shida suka mutu.
Misis Dorries ta ce ta damu matuka kan makomar lafiyar mahaifiyarta mai shekara tamanin da hudu wadda a yanzu haka suke zaune a gida daya.







