Dattawan Arewa sun dage biki saboda coronavirus da kashe-kashe a Kaduna

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta Arewa Consultative Forum (ACF) ta dage wani bikin da ta shirya na cikarta shekara 20 da kafuwa saboda cutar coronavirus da kuma juyayin kisan mutane a jihar Kaduna.

Kungiyar ta ce ta dage taron ne, wanda ta shirya gudanarwa a mako mai zuwa, saboda bullar cutar numfashi ta Coronavirus da kuma kisan sama da mutum 50 da 'yan bindiga suka yi a jihar Kaduna.

Alhaji Musa Liman Kwande shi ne mukaddashin shugaban kungiyar, kuma ya shaida wa BBC cewa za su tara dubban mutane, abinda ka iya janyo yaduwar cutar.

Ya kuma ce bai dace su yi biki ba yayin da ake alhinin kashe-kashe.

"Muna zaton mutum kusan rabin miliyan ne za su taru kuma ganin cewa cutar ta addabi duniya, kada mu tara mutane kuma wasu su tafi gida da tsarabar coronavirus," Musa Liman ya fada wa Ibrahim Isa.

Ya ce sun gayyaci baki daga kasashen waje kamar shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, wanda zai gabatar da makala.

Kazalika, sarakuna da gwamnonin arewa 19 da kuma manyan mutane daga sassan Najeriya duka za su halarci taron, in ji shi.

Alhaji Musa Liman Kwande ya kuma bayyana alhinin kashe-kashen 'yan bindiga a Kaduna a matsayin dalili na biyu da ya sa suka dage bikin.

"Ganin cewa wannan biki za a yi shi ne a Kaduna, inda aka samu asarar rayuka sama da 50, shi ne ya sa muka daga shi."

Ya ci gaba da cewa: "Dole ne mu yi juyayi mu taya 'yan uwan wadanda aka kashe makoki tun da aikinmu a arewa shi ne zaman lafiya da zumunci.

"Saboda haka a kashe mutum 53 a gri guda kuma a gan mu muna yin biki, bai dace da al'adarmu ba da kuma mukami da girman da Allah ya ba mu."

Ya ce nan gaba za su sake saka lokaci domin yin bikin.

An kafa kungiyar ACF ne a shekarar 2000 da nufin hada kan al'ummar yankin arewacin Najeriya kuma tun daga wannan lokaci ne ake jin amonta a al'amuran da suka shafi siyasa da zamantakewa a yankin.