Sabuwar baraka ta kunno kai tsakanin Sarki Sanusi da gwamnatin Kano

Kusan shekara uku kenan ana zaman doya da manja tsakanin masarautar Kano karkashin Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje, amma har yanzu lamarin ya ki ci ya ki cinye wa.

Tun sabanin da rikicin suna zamewa mutane wani sabon labari, a yanzu lamarin ya fara zame wa jama'a jiki.

Tambayar da jama'a suke yi ita ce yaushe za a kawo karshen rikicin kowa ya huta?

Bangarorin gwamnati da suka hada da majalisar dokoki da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen jama'a sun sha kaddamar da bincike kan zargin aikata ba daidai ba kan Sarki Sanusi da Masarautar Kano tun daga watan Afrilun 2017.

Kuma a lokuta da dama binciken na tasowa ne a lokacin da aka samu wata rashin jituwa tsakanin gwamnati da Sarki, abin da kenan yasa wasu ke cewa siyasa ce take haifar da binciken.

Amma hukumomi suna musanta cewa akwai siyasa a cikin abin da suke yi, inda suke cewa suna aiki ne tsakani da Allah kamar yadda dokoki suka tanada.

A ranar Larabar nan majalisar dokokin jihar ta bai wa kwamitinta kan korafe-korafe wa'adin kwana bakwai ya yi bincike kan Sarki Muhammadu Sanusi II dangane da wasu korafe-karafe biyu da aka gabatar mata.

Majalisar ta ce korafe-korafen sun hada da zargin Sarki Sanusi II da yin kalaman da ba su dace da Addinin Musulunci da al'ada ba.

A yayin zaman majalisar na ranar Laraba, shugaban majalisar ya shaida wa 'yan majalisa cewa ''ya karbi korafe-korafen ne daga wata Kungiyar Bunkasa Ilimi da Al'ada ta Kano da kuma wani mutum, Muhammad Mukhtar mazaunin karamar hukumar Gwale a ranar Litinin.''

A ranar ne kuma ita ma hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafen al'umma ta Kano ta fara wani sabon bincike kan zargin karkatar da kudade da ake yi wa Sarki Sanusi II.

Wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC cewa hukumar ta aike da takardar gayyata ga Sarkin na Kano a ranar Laraba.

Hukumar dai tana bukatar Sarkin ya bayyana ranar Alhamis a gabanta domin amsa tambayoyi kan yadda aka sayar da wasu filaye a unguwar Darmanawa mallakin masarautar, aka kuma karkatar da wasu miliyoyin naira.

A duk lokacin da sabuwar takaddama da sabani suka kunno kai, mutane da dama na ganin da alama zaman Muhammadu Sanusi a matsayin sarkin Kano ya zo karshe, ma'ana ana ganin lokacin sauke shi ya zo.

A ganin jama'a da dama manufar duka bincike-binciken ita ce sauke Muhammadu Sanusi daga sarauta.

To sai dai a lokuta da dama ana samun shiga tsakani daga bangarorin al'umma da domin yin sulhu tsakanin gwamnati da Sarki.

Sai dai abin da mutane ke cewa shi ne me ya sa ake kwan-gaba kwan-baya kan wannan batu?

Wasu na ganin cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ake bayyana shi a matsayin mai hakuri, yana da riko kuma ba shi da yafiya idan aka kai shi bango.

A bayyane take cewa Gwamna Ganduje da magoya bayansa suna zargin Sarki Sanusi da goya baya ga dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PDP domin a kayar da Ganduje, zargin da Sarkin ya sha musantawa.

A bangare daya kuma, wasu na zargin Sanusi da rashin kame bakinsa kan wasu manufofin gwamnatin jihar, inda wasu lokutan ya kan futo ya soke su a bainar jama'a, da kuma shigar da gwamnati ko hukumominta kara gaban kotu kan wasu takaddamomi idan sun taso.

An sha yin yunukuri daga ciki da wajen Kano domin ganin an sasanta bangarorin biyu, amma da alama abin ya ci tura.

Bayanan da BBC ta samu a baya-bayan nan sun nuna cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano na cewa tana da kwararan hujjoji da suke nuna zargin aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da kudaden da ya kamata a saka su a asusun masarauta.

Kuma daga karshe dai ''hukumar za ta gurfanar da Sarki a kotu bisa zargin aikata ba daidai ba, wanda hakan zai iya zama dalilin da zai sa a sauke shi daga sarauta saboda kaskantar da masarauta,'' kamar yadda majiyar ta bayyana.

A bayyane take cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ba ta ji dadin hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke ba kan karar da Sarkin ya shigar gabanta ta neman a jingine rahoton hukumar da ya ba da shawarar dakatar da sarki saboda yana kawo tsaiko kan bincike.

Kotun ta jingine rahoton bisa hujjar cewa ba a bai wa sarkin Kano damar kare kansa ba, haka kuma ba a ji ta bakinsa ba.

A lokacin shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa za su yi ''abin da doka ta tanada kamar yadda kotu ta ba da umarni.''

Kuma hakan ne ya kai ga hukumar gayyatar sarkin kano domin ya je ya yi mata bayani kan wasu zarge-zarge.

Idan har sarkin ya je hakan za zama wani kaskanci ne a gare shi, kuma ba a san me zai faru yayin zaman jin bahasin ba.

Idan kuma ya ki zuwa, hakan zai iya zama hujja ga hukumar da gwamnati wajen daukar matakin da suke gani shi ne daidai.

Daya daga cikin wadanda suke yunkurin sasanta bangarorin biyu dai ya ce a wannan karon babu wani abin da za su iya yi, ganin cewa lamarin ya ki ci ya ki cinye wa, sannan magana ce ake yi dangane da bincike.

To amma wani makusancin Sarkin na Kano da bai amince a bayyana sunansa ba, ya ce ba za su ce komai ba tukun, yana mai cewa ''a jira tukun a ga mai zai faru ranar Alhamis, da ake sa ran bayyanar Sarkin gaban hukumar ta Muhuyi Magaji.''

A hukumance dai, masarautar Kano ba ta fitar da sanarwa kan sabuwar takaddamar da ta barke ba, kuma jami'an masarautar ba su amsa kiran da BBC ta yi musu ba kan batun.

Sai dai masarautar Kano da Sarki Sanusi II sun sha musanta duk zarge-zargen.

Wasu dai na ganin duka binciken da majalisar da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi na da nasaba da siyasa, musamman ganin rashin jituwar da ke tsakanin Sarkin Kano da Gwamna Ganduje.