Ganduje ya bai wa Sarki Sanusi awa 48 ya yi bayani kan rashawa

A ranar Alhamis ne rashin jituwa tsakanin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ta kara fitowa fili, bayan da gwamnan ya aike wa da Sarki takardar neman bahasi kan tuhumar da ake yi wa sarkin na yin bushasha da makudan kudaden masarauta.

A ranar Litinin ne dai hukumar karbar korafe-korafen jama'a ta jihar, ta nuna cewa Sarki Sanusi ya yi bushasha da kudin masarauta inda kuma ta nemi da a dakatar da sarkin.

Wani na kusa da Sarki Sanusi wanda ba ya son a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa sun samu takardar neman bayanin, inda a cikinta gwamnati ta bai wa Sarki Sanusi awa 48 da ya bayar da bahasin yadda ya kashe kudaden masarautar.

Ya kuma kara da cewa fadar na nazarin wannan takarda a halin yanzu.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da gwamnatin jihar Kanon ta sanar da soke hawan Nasarawa da sarkin Kano ke yi ranar biyu ga Sallah bisa abin da ta kira harkar tsaro.

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar Laraba ta ce ta samu bayanan sirri da suka nuna cewa akwai yiwuwar samun matsalar saba doka da oda yayin hawan na Nassarawa.

A duk ranar biyu ga sallah ne dai Sarkin Kano yake gudanar da hawan na Nassarawa, inda a yayin hawan yakan ziyarci fadar gwamnati, sannan ya zagaya wasu sassan birnin Kano.

Sanarwar wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Abba Anwar ya sanya wa hannu ta ce an dauki matakin ne bayan taron masu ruwa-da-tsaki kan al'amuran tsaro a jihar ta Kano.

Sanarwar ta ce tuni an sanar da "masarautar cikin birni'' matakin kan rahoton na sirri da kuma soke hawan na Nassarawa.

A nata banagaren masarautar ta Kano ta ce ta samu wannan umarni daga gwamnati, kuma ta janye hawan na Nassarawa da ma hawan Dorayi da ake gudanarwa ranar hudu ga sallah.

Sakataren masarautar ta Kano Malam Awaisu Abbas Sanusi ya shaida wa BBC cewa masarautar ta soke hawan ne bayan samun umarnin gwamnati da kuma son tabbatar da zaman lafiya, da toshe duk wata dama da bata-gari za su iya amfani da ita wajen cutar da al'umma.

An dai fara hawan Nassarawa ne tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka ci Kano da yaki a 1903, inda sarki yake kai wa Baturen mulkin mallaka ziyarar gaisuwar sallah sannan ya yi amfani da damar wajen kewaya wasu sassan birnin Kano, musamman yankunan da baki ke zaune.

Sai dai gabanin sanarwar soke hawan, gwamnatin ta aike wa masarautar Kanon wata takarda inda take sanar da cewa gwamna ba zai samu halartar hawan Daushe ba kamar yadda aka saba saboda wasu dalilai.

Sanarwar wacce ta bulla bainar jama'a ta kuma shaida wa masarautar ta Kano cewa gwamnati ta kuma dage hawan Nassarawa, sai dai a takardar ba a ambaci dalilan tsaro ba.

To sai dai gwamnan da wasu manyan jami'an gwamnati sun jagoranci tawagogi zuwa hawan sallah da sababbin masarautu hudun da gwamnan ya kirkiro suka gudanar.

Wata sanarwa da sakataren watsa labaran na gwamna ya fitar ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa hawan da aka yi a masarautar Bichi.

Shi kuwa mataimakin gwamnan na Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci wata tawagar zuwa hawan da aka yi a masarautar Rano, yayin da shugaban majalisar dokokin jihar Kanon, Kabir Alhasan Rurum ya jagoranci tawagar jami'an gwamnati zuwa hawan da aka gudanar da masarautar Karaye.

Shi kuwa sakataren gwamatin jihar ta Kano Alhaji Usman Alhaji ya jagoranci wata tawagar zuwa masarautar Gaya.

Sai dai babu wani wakilin gwamnati da ya halarci hawan Daushe da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya gabatar a ranar Laraba.

Sharhi daga Yusuf Ibrahim Yakasai

Masu fashin baki dai ba su yi mamaki da matakin gwamnatin na soke hawan na Nassarawa ba, da ma rashin halartar gwamnan Kanon wajen hawan Daushe da aka yi a fadar sarkin Kano ba.

Da ma tun kafin sallah an yi zaton cewa gwamnan na Kano ba zai halarci hawan na Daushe ba, kuma sai ga shi hasashen masu cewa zai je Bichi ne domin hawan ya tabbata.

Wasu ma sun yi mamakin ganin yadda gwamnan ya halarci sallar idi a filin idi na Kofar Mata, wanda mai martaba Sarkin Kano ne yake jagorantar sallar.

Masu irin wannan ra'ayi dai na ganin cewa rashin jituwar da ya fito fili tsakanin gwamnan Kanon da Sarkin Kanon tun bayan zaben 2019 zai iya haifar da matsala.

A ganin masu sharhi da dama matsalar rashin jituwar ita ce ta sa gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiri karin masarautu hudu a jihar Kanon domin zama kishiyiyo ga masarautar Kanon da ke da girma da kasaita.

Tun bayan kirkiro masarautun dai an ga yadda gwamnan Kano ya kulla kawance na kut da kut da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero, wanda da ne ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero kuma na hannun daman Sarki Sanusi kafin a nada shi sarkin Bichin.

Har yanzu dai gwamnatin Kano na cewa babu wani sabani tsakaninta da masarautar Kanon, kuma ta kirkiri masarautun ne domin samar da ci-gaba, to sai dai abubuwan da suke faruwa a zahiri sun nuna sabanin hakan.

Tun bayan nada sababbin sarakunan da Ganduje ya yi, gwamnan na Kano ya ziyarci duka masarautun sama da sau daya, musamman ma dai masarautar Bichi da gwamnan yake kai wa ziyara fiye da sauran.

To sai dai tun daga lokacin, Ganduje bai kai ziyara masarautar Kano ba. Hatta ma lokacin da aka yi saukar tafsirin da ake yi a fadar sarkin na Kano gwamna bai halarci saukar ba, wacce a bisa al'ada gwamnoni kan halarta.

Wani abu da yake kara fito da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu, shi ne rashin halartar Sarki Sanusi II wajen rantsar da Gwamna Ganduje wa'adi na biyu, inda sauran sababbin sarakunan hudu gaba daya suka halarta.

Wasu bayanai da na samu daga wasu na kusa da gwamnati sun tabbatar min da cewa gwamnan Kano ya kullaci Sarkin Kano saboda bai goyi bayansa ba lokacin da Gandujen ya nemi wa'adin mulki na biyu a zaben 2019.

Majiyar ta kara da cewa gwamnati tana da hujjojin da ke nuna cewa Sarkin bai so Ganduje ya sake cin zabe ba, sannan kuma ya taya dan takarar PDP Abba Kabir Yusuf yakin neman zabe a karkashin kasa.

To sai dai gwamnatin ba ta tabbatar da wannan magana ba a hukumance, sannan ita ma masarautar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan zargi.

Sai dai tun bayan zaben an lura da cewa takun gwamnatin Kano ya sauya dangane da Sarkin Kano da masarautar Kanon.

Bayan zaben ne majalisar dokokin Kano ta yi doka a kan kirkirar karin masarautu, kuma gwamna ya sa mata hannu, aka nada sarakunan, aka ba su takarda, sannan aka ba su sanda a cikin kasa da kwana bakwai, abin da wasu ke ganin an yi ne domin cimma wata manufa ta muzguna wa Sarkin Kano.

Sannan daga lokacin ne kuma hukumar karbar korafe-korafe da cin-hanci da rashawa ta jihar KanoN ta sake taso da binciken da ta taba yi kan yadda aka kashe kudin masarautar Kano bayan nada Sarki Sanusi, inda aka yi zargin cewa an kashe kudin ba bisa ka'ida ba tare da yin facaka da kudin da ya haura Naira biliyan uku.

Masarautar ta Kano dai ta musanata zargin, inda tun a wancan lokacin ta yi bayani dalla-dalla kan yadda abin da ke cikin asusun masarautar da kuma yadda aka kashe kudin.

Ko da a wancan lokacin ma dai an fara binciken ne bayan wani rashin jituwa ya kunno kai tsakanin Sarkin da gwamnan kan wasu kalaman da sarkin ya yi kan 'yan siyasa.

Sai dai an warware sabanin a lokacin bayan da wasu manya suka shiga maganar.

To amma a wannan karon bayanai na cewa gwamnan Kanon ya yi kunnen kashi ga duk masu kokarin shiga tsakani da nufin yayyafa wa kurar da ta taso ruwa.

Har yanzu dai gwamnatin Kano ba ta fitar da matsayarta ba kan shawarar da hukumar karbar korafe-korafe ta Kano ta bayar cewa a dakatar da Sarkin Kano Muhammad Sanusi II saboda zargin yana yin katsalandan a binciken kashe kudin masarautar ta hanyar hana duk wadanda aka gayyata domin bayar da shaida gaban hukumar.

Abin tambaya a nan shi ne shin ko a wannan karon ma sarkin na Kano zai tsallake wannan guguwar da ta taso, ko kuwa?