Coronavirus ta shiga Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ta sanar da bullar cutar numfashi ta Covid-19 a karon farko a kasar.

Ministan Lafiyar kasar Zweli Mkhize cikin sanarwar da ya fitar ya ce cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa a kasar ta tabbatar da bullar cutar.

Mutumin da aka samu da cutar mai shekara 38 ya je Italiya ne da mai dakinsa a kwanakin baya.

Suna daga cikin tawagar mutum 10 da suka koma Afirka ta Kudu ranar 1 ga watan nan na Maris.

Mara lafiyar ya je wajen likita ranar 3 ga watan Maris saboda yana fama da alamun zazzabi da ciwon kai da tari da ciwon makogwaro.

Wata ma'aikaciyar jinya ta yi masa gwaje-gwaje kuma tun ranar yake a killace.

Ma'auratan suna da yara biyu. Tuni dai cibiyar ba da agajin gaggawa ta gano mutanen da suka yi mu'amala da shi. Shi ma likitan an kebe shi.

Sanarwar ta kuma ce za a gudanar da taron manema labarai domin yin karin haske game da lamarin a nan gaba.